Gwamnatin Katsina Ta Kare Shirinta Na Sakin Ƴan Ta’adda 70 Daga Gidan Yari

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana dalilin shirinta na sakin wasu mutane 70 da ke fuskantar shari’a, bisa zarginsu da hannu a ayyukan ta’addanci, inda ta bayyana hakan a matsayin wani yunƙuri na ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya da ƙungiyoyin ƴan ta’addan a faɗin jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Nasir Muazu, ya ce; an ɗauki matakin ne da nufin ɗorewar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin al’ummomin da abin ya shafa da kuma ƴan bindigar da suka tuba.

  • Shugabannin Ƙasashe Huɗu Da Amurka Ta Kama Amurka Ta Gurfanar Da shugaban Ɓenezuela Nicolas Maduro
  • Sakin Ƴan Bindiga 70 A Jihar Katsina: Ya Haifar Da Cece-kuce

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon DCL Hausa, a ranar Asabar da ta gabata a daidai lokacin da jama’a ke nuna ɓacin ransu, kan wata wasiƙa da gwamnati ta fitar na neman a sa baki a shari’a domin a sako waɗanda ake tuhuma a halin yanzu.

Ya ce, yarjejeniyar zaman lafiya ta yi sanadin sako mutane kusan 1,000 da aka yi garkuwa da su.

A cewar kwamishinan, aƙalla ƙananan hukumomi 15 ne suka shiga shirin samar da zaman lafiya, wanda a cewarsa; hakan ya sa aka sako mutane kusan 1,000 da aka sace.

Muazu ya kwatanta sakin waɗanda ake zargin da abin da ke faruwa a lokacin yaƙi, inda ɓangarorin da ke faɗa da juna ke musayar fursunoni.

Ma’aikatar shari’a ta Jihar Katsina ce ta fitar da wasiƙar, wadda Sahara Reporters ta fara aikowa da ita zuwa ga babban alƙalin jihar, inda ta buƙaci kwamitin da ke sa ido kan shari’a na manyan laifuffuka (ACJMC) ya sa baki, domin a sako waɗanda ake zargin.

Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun Daraktan Ƙararrakin Jama’a Abdurrahman Umar, ta bayyana cewa; ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta miƙa jerin sunayen mutane 48 da ake zargi da laifuka daban-daban da suka shafi ta’addanci zuwa ma’aikatar shari’a.

Ma’aikatar ta ce, sakin da aka gabatar shi ne ya zama “ɗaya daga cikin sharuɗɗan ci gaba da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu tsakanin ƙananan hukumomi na gaba da ƴan ta’addar.”

Wasiƙar ta kuma bayyana cewa, yayin da aka gurfanar da wasu daga cikin waɗanda ake zargin a gaban babbar kotun tarayya, yawancinsu na ci gaba da tsare a kotunan majistare daban-daban na jihar, suna jiran shari’a.

Har ila yau, an kuma gabatar da jerin sunayen fursunoni kusan 22 da ke fuskantar shari’a a gaban manyan kotuna daban-daban na Jihar Katsina, domin a sake su a ƙarƙashin wannan shirin na zaman lafiya.

Kazalika, Ma’aikatar ta yi kira ga Babban Alƙalin Jihar da ya ɗauki matakin da ya dace, inda ta bayar da misali da sashe na 371(2) na dokar gudanar da shari’ar laifuka ta Jihar Katsina, 2021, wanda ya bayyana ikon kwamitin da ke sa ido kan shari’a.

Yayin da yake kare matakin sakin ƴan ta’addan kimanin 70, Muazu ya ce; yarjejeniyar zaman lafiya ta haifar da sakamako mai matuƙar ma’ana, musamman wajen sako mutanen da aka sace.

Ya ba da misali da alƙaluman waɗanda aka sako daga ƙananan hukumomin da suka haɗa da Sabuwa (310), Bakori (125), Danmusa (60), Dutsinma (62) da Safana (36).

Bugu da ƙari, Kwamishinan ya bayyana cewa; ma’aikatar shari’a ko kotuna, ba su taka wata doka da ake da ita ba, yana mai cewa; duk wanda bai gamsu da hukuncin ba, yana da ƴancin neman haƙƙinsa.

“A duk faɗin duniya, bayan yaƙe-yaƙe, ana yin musayar fursunoni, a lokacin yaƙin basasar Nijeriya, an yi musayar fursunoni, kamar yadda ya faru a tattaunawar da ta shafi Boko Haram.

“Batun ba wai ko batun an aikata wani laifi ko a’a ba, illa kawai tabbatar da zaman lafiya. musayar fursunoni ba wani sabon abu ba ne a tarihin yaƙi da zaman lafiya,” in ji shi.

Sunayen Ƴan Ta’addar Da Za A Saka

Wani jerin sunayen da jaridar Katsina Times, wata jarida ta yanar gizo a jihar ta samu, ya nuna cewa; akwai mata a cikin ƴan ta’adda 70 da za a sako.

Wasu daga cikin sunayen, akwai Hadiza Dije Hauwa’u daga Safana, Gambo Zubairu Faskari, Muntari Yusuf Safana, Yakubu Alhaji Ardo, Tukur Amadu (Liman), İdi Salisu Gaddi, Abdulhayatu Jabiru, Ya’u Buhari da Amadu Rufa’i Anare.

Dole Ne Gwamnati Ta Biya Iyalan Waɗanda Abin Ya Shafa

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, shugaban ƙungiyar ‘Network for Justice’, Abdullahi Hassan Kofar Sauri ya ce, ya kamata gwamnati ta biya diyya ga iyalan waɗanda harin ƴan bindiga ya shafa a jihar.

Ya ce, abin takaici ne yadda Gwamnatin Jihar Katsina da gwamnatin tarayya suka nuna cewa, ba su da hannu wajen tattaunawa da ƴan bindiga.

“Gwamnatin jihar na ƙoƙarin ganin ta saki wasu ƴan ta’adda da aka kama suke fuskantar shari’a a gaban kotu, wannan abu ne da gwamnatin jihar ta ce; ba ta da hannu a ciki, yanzu kuma waɗannan mutanen suna hannunsu.

“Ƴan ta’addan da aka yankewa hukuncin, suna hannun gwamnati, don haka; gwamnati na tsare da su, sannan kuma dole ne a yanke musu hukunci daban-daban.

“Kawai sai ga labarin cewa, an saki kusan 70 daga cikinsu, wannan lamari ne mai matuƙar tayar da hankali, wanda ya sanya mutane da dama cikin damuwa, sai na yi mamaki: me yasa yanzu gwamnatin jihar ta dawo tana cewa; za ta sake su?

“An yanke wa wani laifin kisan kai da ƙona-ƙone, a nan kuma yaya za ka yi da iyalan waɗanda aka kashe, ta wace hanya za ka biya su, shin gwamnatin jihar za ta fito ta ce, tunda mun saki wancan ɗan ta’addan da ya lalata maka gidanka ko ya kashe maka mahaifanka, yanzu za mu ba ka diyyar da ta dace, gwargwadon waɗanda abin ya shafa?

“Amma babu wanda ya ce komai game da lamarin, kuma waɗannan ƴan ta’adda da aka yanke wa hukunci da za a sako za su koma ƙauyuka, dazuzzuka tare da jama’ar yankin, ta yaya za ku daidaita tsakaninsu hakan? Shi ya sa mutane ke nuna shakku da damuwa.”

Sakin Waɗannan Ƴan Ta’adda Na Da Matuƙar Haɗari – Masanin tsaro

Wani masani kan harkokin tsaro, Yahuza Getso, a wata tattaunawa da aka yi da shi, ya bayyana matakin sakin ƴan bindigar a matsayin wata babbar barazana da kuma haɗari ga Jihar Katsina da ma ƙasa baki-ɗaya, inda ya ce; babu wanda zai iya aminta da su.

A cewar tasa, matakin babu gaskiya a cikinsa.

Ya ci gaba da cewa, “Akwai wani gwamna mai ci a halin yanzu daga yankin Arewa-maso-yamma, wanda kwanan nan ya raba babura ashirin da biyar ga ƴan ta’adda, yanzu ku gaya min ina batun gaskiya da jajircewa wajen kawo ƙarshen wannan matsala ta rashin tsaro?

Dawowar Hare-haren Ƴan Bindiga

Matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na ganin an sako ƴan bindiga 70, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a jihar.

A ranar Litinin da ta gabata ne, wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Malumfashi da ke jihar, inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Ƙauyukan da abin ya shafa, sun haɗa da Unguwar Alhaji Barau, Gidan Dan Mai-gizo da Gidan Hazo.

Ya zuwa watan Nuwambar shekarar da ta gabata, ƙananan hukumomi 18 daga cikin 34 na jihar, sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da ƴan bindiga.

Yayin da wasu daga cikin ƙananan hukumomin suka samu kwanciyar hankali, wasu kuma na ci gaba da fuskantar hare-hare, duk da tattaunawar da aka yi, lamarin da ya sanya ayar tambaya game da ingancin yarjejeniyar.

Ƙananan hukumomi 18 da suka shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ƴan bindigar sun haɗa da; Kankara, Kafur, Malumfashi, Funtua, Batagarawa, Charanchi, Sabuwa, Dandume, Faskari, Matazu, Musawa, Safana, Kurfi, Dutsinma, Jibia, Batsari, Danmusa da Bakori.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya, sun yi alƙawarin mutunta sharuɗɗan, yayin da ƴan bindigar suka amince da dakatar da kai hare-hare, tare da sakin waɗanda aka kama.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *