Yadda Za Ku Gyara Kanku

[ad_1]


Da yawa daga cikin mata sun fi son yin amfani da maganin mata wajen gyaran jiki, amma a zahirin gaskiya yin amfani da kayan halitta (organic stuffs) wajen gyara ya fi tabbas, ya fi lafiya, kuma ba ya haifar da illa, sai dai abin yana bukatar tsari da ci gaba da amfani ba kawai a fara a daina ba.

Ga hanya mai sauki da mace za ta bi don samun ingantaccen gyara:

Abubuwan da ake bukata:

Aya, Dabino, Kwakwa, Nonon rakumi, Zuma mai kyau.

Yadda za ki hada:

Ki cire kwallon da ke cikin dabino, sai ki hada kwakwa da aya da dabinon, ki markada su waje daya. Bayan haka, ki kawo zuma mai kyau, mai dan yawa da kuma nonon rakumi kamar kofin shayi daya. Ki hada da kwakwar da kika markada da dabino da aya. Ki juya su waje daya sosai har sai sun hadu.

Yadda ake amfani da shi:

Ki adana hadin a wuri mai tsafta, sannan ki rika sha da safe da yamma.

Idan hadin ya kare, za ki iya sake yin wani. Kada ki yi da yawa domin kada ya lalace kafin ki gama shan sa. Ki yi hadin kamar na kwanaki bakwai kawai.

Wannan hadin na masu aurene.

Don maganin tsatsatsagewar gaba:

Ga mace da take fama da matsalar tsatsatsagewar gaba, ga abin da za ta nema:

Abubuwan da ake bukata:

Manyan kabewa, Ganyen zogale, Man kadanya, Magiji, Garin (na magani)

Yadda ake hadawa:

A hada su waje daya, a kwaba da man kadanya, sai a rika shafawa sau biyu ko uku a rana.

Kowane lokaci da aka shafa, a wanke wurin da ruwan dumi. Da iznin Allah, za a ga canji mai kyau.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *