Darussa Daga Ramadan Na 9: Danne Fushi Da Nutsuwa A Ramalana
A cikin watan Ramalana muna koyon yadda za mu danne zukatanmu daga abin da ya sosa su, mu shawo kan fushi, mu kuma mallaki kanmu a lokacin da ake tsokanar mu. Domin mutum yana ƙara hikima, da dattako, da kwarjini da kwanciyar hankali idan yana cikin nutsuwa.
Azumi ba horon ciki kaɗai ba ne, horo ne na zuciya da hali. Yana koya mana sarrafa motsin rai, musamman fushi. Sau da yawa fushi yana sa mutum ya faɗi kalmomin da zai yi nadama daga baya, ko ya aikata abin da zai lalata dangantakarsa da mutane. Amma Ramalana yana tsayar da mumini a kan turbar natsuwa da tunani da haƙuri.
- Darussa Daga Ramadan Na 8: Haƙuri Da Sadaukarwa Domin Rabauta Ta Har Abada
- Darussa Daga Ramadan Na 7: Farin Ciki Na Gaskiya A Rayuwar Mumini
Manzon Allah (S.A.W) ya koyar da mu wannan tarbiyya a fili. Ya zo a cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim cewa ya ce: “dan ɗayanku yana azumi, kada ya yi maganar banza ko wauta, kuma kada ya yi hayaniya ko sa-in-sa. Idan wani ya zage shi ko ya takale shi da faɗa, to, sai ya ce: ‘Ni azumi nake yi’” Wannan umarni yana da ɗauke da hikima mai girma. Ba wai kawai ka yi shiru ba, har ma ka tuna wa kanka cewa kana cikin ibada. Ka tuna cewa kana azumi domin Allah, don haka; ba za ka bari fushi ya ɓata maka ibada ba.
Fadin “Ni azumi nake yi” yana da ma’ana biyu:
1. Tunatawa kanka cewa kana cikin ibada, don haka; sai ka kame zuciyarka.
2. Kana bayar da saƙo ga wanda ya tsokane ka cewa ba ka shirya shiga rikici ba a wannan lokaci.
Wannan shi ne matakin dattako. Domin wanda ya iya danne fushi, ya fi ƙarfin wanda ya iya rinjayar mutane da ƙarfi. A hakika, ƙarfi na gaskiya ba ƙarfin jiki ba ne, sai dai ƙarfin mallakar zuciya da sarrafa ta cikin hikima.
Ramalana yana gina wa mumini halin juriya da natsuwa. Idan muka iya danne zukatanmu a cikin azumi, to za mu iya yin hakan bayan Ramalana. Za mu iya zama masu haƙuri a gida, masu natsuwa a wurin aiki, masu kamun kai a cikin al’umma.
Danne zuciya ba rauni ba ne; alama ce ta kamalar tunani da dattako. Natsuwa ba gazawa ba ce; alamar hikima ce. Kuma kwanciyar hankali ba kasala ba ce; alamar cikakken imani ce. Saboda haka, mu sanya Ramalana ya zama wata na gyaran hali. Idan an tsokane mu, mu yi shiru. Idan an ɓata mana rai, mu nemi lada a wurin Allah. Idan aka neme mu da faɗa, to mu zaɓi zaman lafiya.
Allah Ya ba mu ikon danne zukatanmu daga fushi, Ya kawata mu da halin natsuwa da hikima, Ya kuma karɓi azuminmu cikin yardarsa. Amin.
Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki