Sojoji sun tallafa wa mutanen Yobe da N23m bayan harin kuskure

[ad_1]



Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bai wa mutanen garin Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe, tallafin Naira miliyan 23 tare da alƙawarin gina rijiyar ruwa mai amfani da hasken rana.

Wannan tallafi ya biyo bayan wani harin kuskure da jiragen yaƙin rundunar suka kai a watan Satumba 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas da jikkata wasu 30.

Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritay), wanda shi ne mai bai wa Gwamna Buni shawara kan harkokin tsaro, ya bayyana cewa wannan tallafi ya nuna tausayin gwamnati da rundunar sojan sama ga al’ummar garin.

Ya ce, tun bayan faruwar lamarin, gwamnan Yobe Mai Mala Buni da Gwamnatin Tarayya suna ƙoƙari wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

A madadin Babban Hafsan Sojin Sama, Komando U.U. Idris na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), ya ce rundunar ta bayar da Naira miliyan 23 ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma naira dubu 500 ga kowane mutum daga cikin waɗanda suka jikkata.

Ya ƙara da cewa, rundunar ta yi wa wadanda suka rasu addu’a, tare da fatan Allah Ya kiyaye faruwar irin hakan a nan gaba.

A nasa jawabin, Alhaji Ali Lawan, wanda ya wakilci al’ummar garin Buhari, ya gode wa rundunar Sojin Sama bisa wannan taimako.

Ya kuma roƙi jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen yaƙar ’yan ta’adda, domin har yanzu yankin na fuskantar barazanar tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *