An rantsar da Mamdani a matsayin Musulmi na farko Magajin Garin New York
[ad_1]
A ranar Alhamis, Zohran Mamdani ya zama magajin garin New York City na farko da aka taba rantsarwa da Alƙur’ani.
Shi ne musulmi na farko kuma dan asalin Kudancin Asiya da ya zama magajin garin birni mafi girma a Amurka.
Mamdani ya yi amfani da Alƙur’ani na kakansa da kuma wani kwafin Alkur’anin mai shekaru 200 da aka aro daga ɗakin karatu na birnin New York a wajen rantsuwar da aka gudanar a tsohuwar tashar jirgin ƙasa ta Times Square.
Ya kuma shirya yin amfani da kwafi biyu na Alƙur’ani da suka kasance na kakansa da kakarsa a wajen bikin rantsuwar da za a yi a ginin majalisar birnin New York City Hall a ranar Juma’a.
Wannan tarihi na Alƙur’ani da aka aro daga ɗakin karatu, ya taɓa kasancewa mallakar Arturo Schomburg, wani marubuci kuma masanin tarihin baƙar fata, wanda ya sayar da tarin littattafansa guda 4,000 ga dakin karatun a shekarar 1926.
Ga wasu daga cikin hotunan rantsuwar da ma na Alkur’anin mai dimbin tarihi:


Masu alaƙa
[ad_2]
Source link