Tirela ta jikkata mutum 87 a Yobe
[ad_1]
Wani hatsarin tirela ya yi sanadiyyar mutuwar fasinja ɗaya tare da jikkatar wasu 87 a kan hanyar Potiskum–Azare da ke cikin ƙaramar hukumar Potiskum a Jihar Yobe.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2: na ranar Laraba a kusa da shataletalen shiga Potiskum, lokacin da tirelar da ke ɗauke da fasinjoji zuwa kasuwar shanu ta Potiskum ta kife.
Bisa ga bayanin waɗanda suka tsira daga hatsarin, tirelar na ɗauke da kusan mutane 100 daga ƙaramar hukumar Katagum ta jihar Bauchi a hanyarsu ta zuwa kasuwar shanu lokacin da lamarin ya faru.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Amir Dauda, wanda ya yi magana daga gadon asibiti, ya ce: “Mun taso daga Azare zuwa kasuwar shanu ta Potiskum. Da muka kusanci shataletalen shiga, direban ya yi ƙoƙarin yin dabara, sai motar ta kife. Mutane suka fara ihu, da dama daga cikinmu suka fada kan juna.”
Lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci sashen gaggawa na Asibitin Kwararru na Potiskum, an ga da dama daga cikin waɗanda suka jikkata kwance a ƙasa saboda ƙarancin wuri a sashen gaggawa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar hatsarin da kuma adadin waɗanda suka mutu da suka jikkata.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link