Gwamnan Filato Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
[ad_1]
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance. Mutfwang ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban PDP na mazaɓarsa ta Ampang West, Dasjak Sunday Longyol, mai ɗauke da kwanan wata 29 ga Disamba, 2025.
A cikin wasiƙar, gwamnan ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne domin neman wani dandalin siyasar da zai ba shi damar yi wa Jihar Filato hidima yadda ya dace. Ya kuma nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na shiga harkokin dimokuraɗiyya.
- ‘Yan Bindiga Sun Rage Kuɗin Fansar Matafiya 28 Da Suka Sace A Filato zuwa N30m
- Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Ƙungiyar Da Ke Safarar Makamai Tare Da Kama Mutane 3 A Filato
Mutfwang ya bayyana cewa shawarar ta samo asali ne daga jajircewarsa kan shugabanci mai ma’ana, da fayyace alkibla da kuma inganta yi wa al’umma hidima. Ya gode wa shugabannin jam’iyya, da mambobi da magoya baya a dukkan matakai bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake cikin PDP.
Sai dai gwamnan bai bayyana jam’iyyar da yake shirin komawa ba. Wannan mataki nasa ya zo ne bayan jita-jitar da ta shafe watanni ana yaɗawa cewa Mutfwang na shirin komawa jam’iyyar APC, lamarin da ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Filato.
[ad_2]
Source link