Wasu Jiragen Yaƙin Amurka Sun Faɗo A Kuwait – Ma’aikatar Tsaro
[ad_1]
Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar Kuwait ta bayyana a ranar Litinin cewa, wasu jiragen yaƙin Amurka sun faɗo cikin ƙasar, sai dai dukkanin ma’aikatan jiragen sun tsira da rayukansu.
Har yanzu ba a bayyana ainihin adadin jiragen da lamarin ya shafa ba, haka kuma ba a san musabbabin faɗuwar jiragen ba. Rahotannin kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun nuna cewa, watakila makaman Iran ne suka harbo jiragen, a yayin da yaƙi ke ci gaba tsakanin Amurka da Iran. Bidiyon da Al Jazeera ta fitar ya nuna ɗaya daga cikin jiragen yaƙin na faɗowa.
- An Kashe Manjo Da ‘Yan Ta’adda 10 A Hare-haren Da Aka Daƙile Kan Sansanonin Soja
- Ina Cikin Masu Neman Horar Da ‘Yan Wasan Nijeriya Yan Ƙasa Da Shekaru 17 – Sani Kaita
Kuwait na daga cikin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da hare-haren makamai masu linzami na Iran suka shafa, inda aka kai hari kan sansanonin sojojin Amurka da muhimman cibiyoyi. Sauran ƙasashen da rahotanni suka ce an kai wa hari sun haɗa da Qatar, Bahrain, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da Saudiyya.
Amurka ta tabbatar da cewa, sojojin Amurka uku sun mutu, yayin da aƙalla wasu biyar suka jikkata sosai sakamakon hare-haren.
Rikicin ya ƙara tsananta ne a ranar Asabar lokacin da dakarun Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran. Tun daga lokacin ne Iran ta fara mayar da martani ta hanyar kai hare-haren makamai masu linzami kan wuraren Amurka da Isra’ila a yankin.
[ad_2]
Source link