Tinubu, Shettima Zasu Ziyarci Kano Halartar Tarɓar Gwamna Yusuf Zuwa APC

[ad_1]

Jihar Kano na shirin karɓar manyan jiga-jigan siyasa yayin da jam’iyyar APC za ta yi babbar tarba ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan shigarsa jam’iyya mai mulki.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da gwamnoni da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC za su halarci taron.

  • Rundunar Tsaro Ta Kano Ta Kama Haramtattun Magunguna Na Naira Biliyan 1.5
  • Yadda Sakataren Jam’iyyar APC Na Ƙasa Ya Ziyarci Gwamna Abba Kabir Yusuf

Wuri da Lokaci

An shirya gudanar da taron ne ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, a Sani Abacha Stadium, Kofar Mata, Kano. Ana sa ran taron zai ja hankalin dubban magoya baya da manyan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Muhimmancin Taron

Wani jigo a jam’iyyar ya bayyana taron a matsayin babban mataki ga APC a Kano, wadda ake kallonsa a matsayin jiha mai muhimmiyar rawa a taswirar siyasar Nijeriya. Ya ce taron zai ba jam’iyyar damar nuna ƙarfi da haɗin kai a yankin Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

Shirye-shirye da Kwamitoci

Domin tabbatar da nasarar taron, an kafa muhimman kwamitoci kamar haka:

Kwamitin Tsaro (mambobi 15): Ƙarƙashin jagorancin Col. Umar Malami, tare da Darakta-Janar na Special Service a matsayin sakatare.

Kwamitin Lafiya da Tsabtace Muhalli (mambobi 15): Dr. Abubakar Labaran ne ke jagoranta, yayin da Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ke matsayin sakatare.

Kwamitin Wuri (mambobi 16): Hon. Bala Mohd Gwagwarwa a matsayin shugaba, Engr. Umar Abdullahi Ganduje sakatare.

Kwamitin Yaɗa Labarai (mambobi 15): Hon. Muhammad Garba shugaba, Hon. Sunusi Bature Dawakin Tofa sakatare.

Kwamitin Tsari da Ladabi (mambobi 15): Hon. Abdullahi Rogo shugaba, Hon. Ibrahim Zakari Sarina sakatare.

Kwamitin Wayar da Kai da Tattara Jama’a (mambobi 20): Hon. Mohd Bello Butu-Butu shugaba, Hon. Ma’aruf Abdullahi Garo sakatare.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *