Ministan Wajen Sin Zai Ziyarci Kasashen Afirka Hudu Tare Da Halartar Wani Biki A Hedkwatar AU
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai ziyarci kasashen Habasha, Somaliya, Tanzania da Lesotho bisa gayyatarsa da aka yi, daga ranar 7 zuwa 12 ga Janairu, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a yau Laraba.
Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, zai halarci bikin kaddamar da shekarar musayar cudanyar jama’a tsakanin Sin da Afirka a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka (AU). A cewar sanarwar, shekarar 2026 ita ce ta cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Afirka.
Ziyarar Wang zuwa kasashen Afirka hudu da kuma halartar bikin kaddamar da shekarar musayar cudanyar jama’a tsakanin Sin da Afirka na ci gaba da kasancewa al’adar ministan harkokin wajen kasar Sin ta zabar Afirka ta zamo farkon wurin ziyara a waje kowace shekara, a cikin shekaru 36 da suka gabata, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning ta bayyana a wani taron manema labarai a yau Laraba.
Ta kara da cewa, Habasha, Somaliya, Tanzania da Lesotho dukkansu abokan hulda ne na kasar Sin a matakin manyan tsare-tsare, kuma makasudin ziyarar Wang shi ne zurfafa amincewa da juna a siyasance tare da dukkan nangarorin.
Mao ta kuma ce, ziyarar tana da nufin karfafa aiwatar da sakamakon taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, da karfafa koyo daga juna a tsakanin Sin da Afirka a matsayin masu manyan wayewar kai guda biyu, da kuma kara sanya sabon kuzari ga gina al’ummar Sin da Afirka ta dukkan fannoni mai makoma ta bai-daya a sabon zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link