An Dakatar Da Kocin Manchester City Pep Guardiola Daga Buga Wasanni Biyu

[ad_1]

Mahukuntan gasar Firimiya ta kasar Ingila sun dakatar da kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola daga buga wasanni biyu da suka hada da wasan da zasu buga da West Ham United a gasar Firimiya da kuma wasan zagayen na kusa da na karshe na gasar FA Cup da zasu buga a watan Afirilu.

Hakan ya biyo bayan katin kora da ya samu a wasan da Manchester City ta doke Newcastle United da ci 3-1 a gasar cin kofin FA da suka buga ranar Asabar, wannan ne karo na shida da aka bai wa Guardiola katin gargadi a wannan kakar, lamarin ya faru ne bayan da tsohon kocin na Barcelona ya yi cacar baki da alkalin wasa na hudu, Lewis Smith bayan da Kieran Trippier ya yi wa Jeremy Doku na City keta.

Yanzu kenan Guardiola ba zai halarci wasan kungiyar da West Ham a filin wasa na London Stadium a gasar Premier ranar Asabar mai zuwa ba da kuma wasan kusa da na karshe na gasar FA a watan Afrilu, duk da haka dakatarwar ba ta shafi wasannin gasar zakarun Turai ba, don haka za a bar Guardiola ya shiga filin wasa a wasan da zasu buga da Real Madrid a gasar zakarun Turai da kuma wasan karshe na Carabao da zasu buga da Arsenal a ranar 22 ga watan Maris.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *