Trump ya halarci bikin karɓar gawarwakin sojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya halarci bikin karɓar gawarwakin sojojin Amurka shida na farko da suka mutu a rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Amurka da Iran.

An sauke gawarwakin sojojin ne ranar Asabar a sansanin sojin sama na Dover, inda ake karɓar gawarwakin sojojin Amurka da suka mutu a ƙasashen waje kafin a kai su wajen shirya jana’iza.

Trump ya yi gaisuwar karramawa tare da sarawa yayin da sojoji ke sauke akwatunan gawarwakin da aka rufe da tutar Amurka daga jirgin soji.

Shugaban ya samu rakiyar uwargidansa Melania Trump, da mataimakin shugaban kasa, JD Vance, da Sakataren Tsaro, Pete Hegseth, da shugaban hafsoshin sojojin Amurka Dan Caine, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Rahotanni sun ce sojojin shida — maza biyar da mace guda — sun mutu ne a ranar Lahadi bayan wani jirgin yaƙi maras matuƙi ya kai hari kan wani muhimmin sansanin sojin Amurka a Kuwait.

Lamarin ya faru ne kwana guda bayan da Amurka tare da Isra’ila suka ƙaddamar da manyan hare-haren soji kan Iran.

Sojojin da suka mutu mambobi ne na rundunar ajiyar soji ta 103rd Sustainment Command da ke hedikwata a Des Moines, wadda ke da alhakin samar wa sojoji abinci, mai, kayan aiki da alburusai.

Karɓar gawarwakin sojojin Amurka — wanda ake kira dignified transfer — na ɗaya daga cikin muhimman al’adu na soji da shugaban Amurka kan halarta domin girmama waɗanda suka mutu a bakin aiki.

Harin da ya kashe sojojin ya ƙara nuna haɗarin da sojojin Amurka ke fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da Iran ke ci gaba da harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan sansanonin Amurka da ƙawenta a yankin.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta kai wa Iran hare-hare masu tsauri kuma za ta faɗaɗa hare-haren zuwa wasu sabbin wurare idan rikicin ya ci gaba da tsananta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *