Sin Za Ta Himmatu Wajen Fadada Cimma Moriya Daga Fasahar AI
Ministar ma’aikatar kula da albarkatun kwadago da kyautata walwalar al’umma ta kasar Sin Wang Xiaoping, ta ce mahukuntan kasar za su kara azamar aiwatar da matakan cimma moriya daga fasahar kirkirarriyar basira ko AI, wajen fadada damammakin samun guraben ayyukan yi, da karfafa cimma gajiya daga ayyuka da aka saba gudanarwa.
Wang, wadda ta bayyana hakan ga manema labarai a Asabar din nan, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana yanzu haka, ta ce ana fatan bude babukan samar da ayyukan yi a fannonin raya tattalin arziki na dijital, da na kirar manyan hajojin masana’antu da hidimomi na zamani.
Ministar ta kara da cewa, ma’aikatarta za ta ci gaba da kara azamar bunkasa sabbin fannonin sana’o’in zamani, tare da mayar da hankali ga fannonin karfafa sarrafa hajoji masu inganci, da sabbin dabarun bunkasa sayayya da hidimomin kyautata rayuwar jama’a.
Ta ce cikin shekaru biyar da suka gabata, ma’aikatarta ta gano sabbin sassan ayyukan yi 72, ciki har da sama da 20 masu nasaba kai tsaye da fasahar AI. Kuma duk fanni daya a matakinsa na farko-farko, na iya samar da guraben ayyukan yi ga jama’a sama da 300,000 zuwa 500,000. (Saminu Alhassan)