AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe
[ad_1]
Shirin AGILE, ya raba kayan koyarwa da na sana’o’i ga cibiyoyin karatun boko na wucin gadi guda 54 a faɗin Jihar Gombe.
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Dakta Aishatu Umar Maigari, ce ta ƙaddamar da rabon kayan a cibiyar Community Education Resource Centre da ke Gombe.
Ta ce manufar shirin shi ne bai wa ɗalibai damar koyon karatu, lissafi da kuma sana’o’i domin su samu rayuwa mai inganci.
“Ba wai kawai karatu muke son su samu ba, har da ƙwarewar sana’a da za ta taimaka musu da iyalansu,” in ji ta.
Shugabar shirin AGILE ta jihar, Dakta Amina Haruna Abdul, ta ce wannan tallafi zai ƙara wa ɗalibai ƙwarewar da za su yi amfani da ita wajen ci gaban al’umma.
Ta roƙi shugabannin cibiyoyi da malamai su kula da kayan, su kuma tabbatar an yi amfani da su yadda ya dace.
Wannan tallafi da ya shafi cibiyoyi 54 ana sa ran zai bunƙasa ilimin boko na wucin gadi ta hanyar haɗa karatu, lissafi da koyon sana’o’i a waje guda.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link