Dimokuradiyya Mai Tsarin Al’umma Baki Daya: Wata Aba Ce Mai Yiwuwa A Siyasar Wayewar Kai Ta Bil Adama

[ad_1]

Chen Junqing, mai shekara 82 da haihuwa daga birnin Xiangxiang na lardin Hunan na kasar Sin, ya shiga damuwa sosai bisa yadda jikansa yake fama da ciwon ciki, saboda yawan cin abincin da ake sayarwa a kan titi.

Bisa damuwar da ya shiga game da ingancin abincin da yara ke ciki, a ranar da ake rufe karbar ra’ayoyin al’umma game da daftarin “dokar kula da kananan harkokin sarrafa abinci da cibiyoyin sarrafawa, da kananan shagunan cin abinci da kuma masu sayar da abinci a lardin Hunan” cikin watan Satumbar 2024, cikin gaggawa ya rubuta shawara kan wata doka mai kunshe da kalmomi 120 a bayan kwalin taba sigari tare da mika ta.

Jigon shawarar shi ne a kara tsananta hukuncin ladabtarwa ga masu samar da abinci da masu aikin gudanarwa wadanda suka kasa cika ka’idojin ingantacciyar tsafta. Wannan shawarar, daga karshe ta samu amincewar zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’a ta lardin Hunan kuma ya sanya ta cikin sashe na 40 na sabbin dokokin da aka yi wa kwaskwarima.

Wannan ba wani lamari ne da ya kasance kebantacce ba, amma wata fa’ida ce ta dimokuradiyya irin ta kasar Sin. Wannan nau’i na dimokuradiyya na musamman, wanda aka fi sani da “dimokradiyya mai tsarin al’umma gaba daya,” yana bayar da sabuwar kafa ta yiwuwar samun siyasar wayewar kai ta bil’adama. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *