Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya
Yayin da aka karkare manyan tarukan siyasa biyu na kasar Sin, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar Sin NPC, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC na bana, masharhanta da suka shaida abubuwan da aka tattauna yayin tarukan, sun jinjinawa kwazon kasar Sin ta fuskar aiwatar da manufofin samar da ci gaba mai inganci, da yadda kasar ta himmatu wajen tattauna dabarun tsara ayyuka na dogon lokaci, wadanda dukkaninsu ke zama muhimman ginshikai na daidaita yanayin ci gaban duniya baki daya.
Baya ga muhimmin aikin nazari, da zartar da daftarin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da kasar za ta aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2026 zuwa ta 2030, wani muhimmin bangare na tasirin tarukan shi ne tsara manufofi daga bangaren Sin, wadanda za su karfafa daidaiton ci gaban duniya baki daya.
La’akari da ayyuka daban daban da tuni gwamnatin Sin ke gudanarwa, mun shaida yadda kasar ke shigar da sabon kuzari a fannin bincike da samar da ci gaba, da bullo da dabarun samar da ci gaba mai inganci, wadanda muhimman ginshikai ne cikin shirin na raya kasa karo na 15.
Ko shakka babu, wannan shiri na raya kasar Sin ya tabbatar da alkiblar kasar ta gaggauta rungumar sabon tafarkin bunkasa masana’antu ta amfani da fasahohi, da kirkire-kirkire da kere-keren zamani.
A ganina, matsayin da kasar Sin ke kai a halin yanzu, na shige wa gaba wajen jagorantar samar da hajoji masu inganci, da kakkarfan ikon zuba jari a masana’antun dijital, da sauran muhimman fannoni, zai wanzar da kasar a matsayin ginshikin ingiza sabon sauyin da duniya za ta samu a fannin fasahohin zamani cikin shekaru da dama masu zuwa.
Har ila yau, a babin misali, manufofin samar da ci gaba irin su shawarar ziri daya da hanya daya, wadanda ake kokarin daidaita tafiyarsu da ajandoji irin na raya ci gaba Afirka nan zuwa shekarar 2063, za su tabbatar dabarun ci gaba na sassan duniya mabanbanta, sun ci gaba da karfafa juna.
A takaice, muna iya cewa wadannan manyan tarukan siyasa biyu na kasar Sin, sun baiwa duniya wata kofa ta kara fahimtar gudummawar Sin ga raya ci gaban duniya na bai daya, da ma kyakkyawar aniyar kasar ta ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya.