Babban limamin Ilorin ya rasu
[ad_1]
Babban Limamin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kwara, Sheikh Bashir Solihu, ya rasu yana da shekara 75 a duniya.
Shugaban Ƙungiyar Masu Yaɗa Addinin Musulunci (IMAN), Sheikh Abdullahi Nurudeen-Adana, ne ya tabbatar da rasuwar Babban Limamin a ranar Litinin.
Nurudeen-Adana, wanda ya yi magana da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a Fadar Sarkin Ilorin, ya ce marigayin ya rasu ne bayan fama da wata jinya, sai dai bai yi ƙarin haske kan cutar ba.
A cewarsa, Sheikh Bashir Solihu ya shafe shekaru masu yawa yana karantarwa da hidimar addinin Musulunci, lamarin da ya kai shi zama ɗaya daga cikin fitattun shugabannin addini a Jihar Kwara.
Marigayin ya kasance Babban Limami na 12 a masarautar Ilorin, muƙamin da ya riƙe tsawon fiye da shekaru 40, tun bayan naɗa shi a shekarar 1983.
Shugaban IMAN ya bayyana rasuwar Babban Limamin ta girgiza su kuma babban rashi ne ga addinin Musulunci.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga Mai Martaba Sarkin Ilorin, mambobin Majalisar Malamai ta Jihar Kwara, da al’ummar masarautar Ilorin baki ɗaya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link