Sin Da EU Sun Amince Da Batun Kayyade Farashin Motoci Masu Amfani Lantarki Na Kasar Sin

[ad_1]

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, an samu ci gaba dangane da tattaunawar da ake yi tsakanin Sin da kungiyar Tarayyar Turai (EU), kan motoci masu amfani da lantarki na Sin din, kuma bangarorin biyu sun yi ta tuntubar juna ne bisa ka’idojin mutunta juna. Har ila yau, bangarorin biyu sun amince cewa ya zama wajibi a samar da wasu ka’idojin kayyade farashi ga Sinawa masu fitar da motoci masu amfani da lantarki zuwa kungiyar Tarayyar Turai.

A don haka, EU ta gabatar da wani daftarin yarjejeniyar kayyade farashi, inda cikinsa ta tabbatar da cewa, za ta yi biyayya ga ka’idojin da suka shafi rashin nuna wariya da amfani da dokoki iri daya kan kowanne farashi da aka sanya, bisa tanade-tanaden hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, sannan za ta gudanar da nazarce-nazarce bisa gaskiya da daidaito.

Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta kara da cewa, ci gaban da aka samu a tattunawar ta nuna cewa Sin da EU za su iya warware duk wani sabani a tsakaninsu ta hanyar shawarwari da tattaunawa, karkashin ka’idojin hukumar WTO. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *