Kocin Atletico Madrid ya nemi afuwar Vinicius
[ad_1]
Kocin Atletico Madrid, Diego Simeone, ya nemi afuwar ɗan wasan gaban Real Madrid, Vinicius Junior, bayan taƙaddamar da ta shiga tsakaninsu a wasan da aka fafata a gasar Spanish Super Cup.
Simeone ya samu saɓani da Vinicius lokacin da aka sauya ɗan wasan na Brazil a yayin wasan kusa da na ƙarshe da Atletico ta sha kashi da 2-1 a hannun Real Madrid ranar Alhamis.
Haka kuma, kocin ɗan asalin Argentina ya kuma nemi afuwar shugaban ƙungiyar Real Madrid, Florentino Perez, bayan an ji shi yana furta kalamai da ke nuna kamar yana faɗa wa Vinicius cewa shugaban ƙungiyar zai iya korar sa daga kulob ɗin.
“Ina neman afuwar Florentino da Mista Vinicius kan abin da ya faru,” in ji Simeone yayin taron manema labarai gabanin wasan Atletico da Deportivo La Coruna a zagaye na 16 na Copa del Rey.
“Ba daidai ba ne na tsinci kaina a irin wannan yanayi, kuma tabbas na yi kuskure,” in ji shi.
Vinicius Junior ya zura ƙwallo a wasan ƙarshe na Super Cup, amma Real Madrid ta sha kashi da 3-2 a hannun Barcelona.
Kwantaragin Vinicius da Real Madrid zai ƙare ne a watan Yunin 2027, kuma har yanzu bai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da kulob ɗin ba.
[ad_2]
Source link