’Yan bindiga sun sace mutum 170 a wani harin majami’u a Kaduna

[ad_1]



’Yan bindiga sun sace sama da masu ibada 170 a wani hari da suka kai kan wasu majami’u a unguwar Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Shaidu sun ce maharan sun afka wa majami’un ne a yayin da ake tsaka da gudanar da ibada a ranar Lahadi, a majami’un ECWA da Cherubim da Seraphim.

Majiyoyi sun bayyana cewa daga bisani wasu mutum 9 masu rauni daga cikin waɗanda aka sace, sun samu nasarar dawowa gida.

Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Arewacin Nijeriya (CAN), Fasto Joseph John Hayab, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin wanda ya bayyana a matsayin abin takaici da tayar da hankali.

Ya ce, “Ba ma na son na yi magana kan alƙaluman, amma bayanan da na samu daga yankin sun nuna cewa mutane 172 aka sace, mutum tara sun tsere, yayin da sauran 163 har yanzu ke hannu,” in ji shi.

Fasto Hayab ya ƙara da cewa duk da tsananin damuwar da lamarin ya haifar, Kiristocin yankin ba za su yi kasa a gwiwa ba.

“Abu ne mai matuƙar firgici da baƙin ciki, amma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba. Za mu ci gaba da bai wa hukumomin tsaro da gwamnati haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi wajen dawo da zaman lafiya a Kaduna, kuma muna yaba musu,” in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa za su ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro da gwamnati domin tabbatar da cewa an kuɓutar da waɗanda aka sace lafiya.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, gwamnatin Jihar Kaduna da rundunar ’yan sandan jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *