Manyan Kurakuran Sanae Takaichi A Tarihi

[ad_1]


Kwanan nan, firayim ministar Japan Sanae Takaichi ta furta wasu kalaman kuskure game da yankin Taiwan na kasar Sin, wadanda suka yi matukar girgiza duniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ma’aikatar tsaron kasar, kana da ofis mai kula da harkokin yankin Taiwan, da ofishin jakadancin Sin dake Japan sun bayyana rashin amincewa da kakkausar murya bi da bi, yayin da al’ummar Japan su ma suka nuna takaici matuka, har wasu suka yi zanga-zangar neman hambarar da ita.

Alal hakika, kalaman kuskuren da Takaichi ta furta game da Taiwan sun samo asali ne daga tsattsauran ra’ayin da ta kan dauka.

Da farko dai, ta yi watsi da “Sanarwar Murayama” da “Sanarwar Kono”. A shekarar 1994, a matsayinta na ‘yar majalisar kafa dokokin kasar Japan, Takaichi ta yi wa firayim minista mai ci na wancan lokaci Tomiichi Murayama tambaya a majalisa, game dalilin da ya sa ya amince da yakin mamaya da Japan ta yi ba daidai ba ne. Bugu da kari, ta keta “Sanarwar Kono”. A ganinta, Japan ba ta tilastawa mutanen yankin Koriya shiga Japan ba, kana ta musanta mugun tarihin Japan na tilasawa mata ’yan Koriyar shiga karuwanci”.

Na biyu, ta sha kai ziyara gidan haikalin Yasukuni, tare da bayar da shawarar bunkasa karfin soja. Takaichi ta nemi a soke sashen “yin watsi da yaki” a cikin kundin tsarin zaman lafiya na mulkin kasar Japan, da kuma canjar rundanar Japan zuwa “sojojin tsaron kasa”. Tana mai ba da shawarar kara kudin tsaro fiye da kima, don Japan din ta samu karfin kai hari ga sansanonin soja na abokan gaba.

Na uku, bayan ta yi ta ba da shawarar cewa “lamarin Taiwan” zai haifar da hadari ga rayuwar al’ummar Japanawa, a watan Afrilu na wannan shekarar kuma ta ziyarci yankin Taiwan ba bisa tushen gaskiya ba, a matsayinta na ‘yar majalisa, inda ta ba da shawarar “karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin Japan da Taiwan”, da kuma kafa “dangantakar kusa da kawance”.

Binciken ya nuna cewa, manufofin Takaichi suna bayyanawa a fili cewa, ba ta kula da zaman rayuwar jama’a, ta zama ‘yar amshin shatan Amurka, kuma tana kokarin fadada karfin sojan kasarta. Tabbas, kasancewar Takaichi a matsayin firayim ministar Japan shi ne ainihin jigon rikici ga rayuwar Japanawa. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *