Kotu Ta Ɗage Shari’ar Zargin Ta’addanci Da Mallakar Makamai Kan Malami Da Ɗansa Zuwa Afrilu

[ad_1]

Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da ake yi wa tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdulaziz Malami, zuwa ranar 15 da 16 ga Afrilu.

Dukkan waɗanda ake ƙara sun halarci kotun lokacin da shari’ar ta zo gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik.

  • Kamfanonin Sin Sun Gudanar Da Taron Bayar Da Tallafi A Masar
  • APC Na Da Gwamnoni 31 Bayan Sauya Sheƙar Gwamnan Zamfara

A yayin zaman kotun, lauya mai kare gwamnati, Mista Akinlolu Kehinde, SAN, ya sanar da kotun cewa, a ranar Litinin ne aka ba shi umarnin ya karɓi jagorancin shigar da ƙarar, don haka yana buƙatar lokaci domin ya gana da shaidun da za su ba da shaida.

Ya ce: “Na samu umarnin karɓar jagorancin shigar da ƙarar ne a ranar Litinin, don haka ina buƙatar lokaci domin na tattauna da shaidun. Ina roƙon kotu cikin girmamawa da ta ba mu wani sabon lokaci.”

Lauyan da ke kare waɗanda ake ƙara, Mista Shuaibu Arua, SAN, bai yi jayayya da buƙatar ɗage shari’ar ba.

Daga nan sai Mai shari’a Abdulmalik ta amince da buƙatar, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 15 da 16 ga Afrilu domin ci gaba da sauraron shari’ar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *