Ministan Wajen Kasar Sin: Ya Zama Wajibi A Yi Adawa Da Duk Wasu Hare-hare Kan Fararen Hula Da Wuraren Da Ba Na Soji Ba

[ad_1]

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce ya wajaba a martaba ikon mulkin kai, da tsaro da hurumin yankunan dukkanin kasashen duniya, kuma dole ne a yi adawa da duk wasu hare-hare kan fararen hula, da wuraren da ba na soji ba.

Wang ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaran aikinsa na kasar Bahrain Abdullatif bin Rashid Al Zayani. Inda ya ce abubuwan dake kan gaba, su ne gaggauta dakatar da dauki ba dadi tsakanin rundunonin soji, domin dakile bazuwar tashin hankalin da ake ciki.

Wang Yi ya kara da cewa, jakadan musamman na gwamnatin kasar Sin dangane da batun gabas ta tsakiya, ya fara ziyartar sassan kasashe masu ruwa da tsaki a yakin, inda nan gaba zai ziyarci Bahrain, kana kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar gani wajen kare zaman lafiya da daidaito a yankin Gulf.

Kazalika, yayin zantawarsa da takwaran aikinsa na kasar Kuwait, Jarrah Jaber Al-Ahmad Al-Sabah duk dai a jiyan, Wang, ya ce babban burin da aka sanya gaba a yanzu, shi ne cimma nasarar dakatar da bude wuta cikin sauri. Ya ce kasar Sin ta gamsu da kiraye-kirayen da kasashen Gulf ke yi, na a komawa teburin shawarwari da tattaunawa. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *