Cinikin Kasar Sin a Watanni 2 Na Farkon Bana Ya Karu Da 18.3% Idan Aka Kwatanta Da Na Shekarar Da Ta Gabata
[ad_1]
Tun farkon wannan shekara, cinikin shige da fice na kasar Sin ya ci gaba da tafiya ba tare da tangarda ba tare da samun ci gaba, kuma karfin juriya da kuzarinsa ya kara bayyana.
A yau Talata hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana alkaluman cinikin, inda ta nuna cewa, a watanni 2 na farkon wannan shekara, sassa da hukumomi daban-daban sun dauki matakai da himma, kuma kamfanonin masu jarin waje da dama sun yi kokarin tabbatar da samar da kaya, da kuma fadada kasuwanni, yayin da cinikayyar shige da fice ta kasar Sin ta karu da kashi 18.3%, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wanda ke nuna kyakkyawan yanayi na shiga wannan shekara.
Masana sun bayyana cewa, samun “kyakkyawan mafari a bangaren ciniki” a kasar Sin a shekarar 2026, ya samo asali ne sakamakon hadakar dalilai guda 4: Wato farfadowar bukatu a duniya, da bayyanar fa’idodin manufofi a fili, da bayyanar fifikon masana’antu, da kuma karuwar kuzarin kananan hukumomi da daidaikun mutane.
A lokaci guda kuma, ya kamata a lura da cewa, har yanzu ana fuskantar rashin tabbaci da sauye-sauye, musamman ma karuwar tashe-tashen hankula na yanki a kwanan nan, wanda ke kawo babbar matsala ga tsarin samar da kayayyaki a duniya. Ya kamata a baiwa ciniki tabbaci, ta dogaro da kara inganta kirkire-kirkire, da kuma kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a yanayin ciniki da inganta tsarinsa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link