APC Ta Shirya Karɓar Gwamna Yusuf — Abdullahi Abbas

[ad_1]

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta ce ta shirya karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar kafin ficewar sa daga Jam’iyyar NNPP.

Shugaban APC na Kano, Yarima Abdullahi Abbas, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 29 ga Disamba, 2025.

A cewar Abbas, an ɗauki wannan matakin ne don samar da haɗin kai da sulhu a Jihar Kano.

“Wannan matakin yana nufin hadin kai, sulhu da ciyar da Jihar Kano gaba,” in ji shi.

Abbas, wanda ke magana a madadin tsohon shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce APC ta shirya tarbar Yusuf da sauran mambobin NNPP a hukumance, ciki har da ‘yan majalisa, ‘yan majalisar zartarwa na jiha, shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli da kuma wadanda ke riƙe da muƙaman siyasa.

Ya kara da cewa, za a gudanar da liyafar da aka shirya “cikin yanayi na girmama juna da mutuntawa.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *