Karin Kasashe Na Nuna Adawa Da Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Da Goyon Bayan Hadewar Kasar Sin

[ad_1]

Ana samun karuwar yawan kasashe da ke tare da kasar Sin, da sake jaddada alkawarinsu ga bin ka’idar kasar Sin daya tilo a duniya, inda suke kara shaida cewa Taiwan wani bangare na Sin da ba za a iya raba su ba, da kuma nuna adawa da duk wani yunkurin ‘yan aware a kan ‘yancin kan Taiwan, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yau Talata.

Wang ya yi wannan furucin ne lokacin da yake jawabi a wani taron kara wa juna sani kan yanayin kasa da kasa da kuma dangantakar kasar Sin da kasashen waje a shekarar 2025.

Da yake sake nanata cewa batun Taiwan al’amari ne da ya shafi cikin gidan kasar Sin kuma mai muhimmanci a cikin muradun Sin, Wang ya ce abu ne da ya zama dabi’a ta asali ga kasar Sin ta nuna adawa mai tsanani kuma ta dauki matakai masu karfi na mayar da martani a kan masu neman tayar da zaune tsaye kan “‘yancin kan Taiwan” da kuma shirin sayar da makamai masu yawa ga Taiwan daga Amurka.

A yau Talata ne dai, ministan harkokin wajen na Sin Wang Yi, ya yi kira da a kare nasarar da aka samu cikin jibin goshi a yakin duniya na biyu ta hanyar zubar da jini, da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu bayan shan bakar wahala.

Ya kara da cewa, kasar Japan, wacce ta kaddamar da yakin zalunci a kan kasar Sin, ta kasa yin tunani mai zurfi a kan laifukan da ta aikata, kuma har ma shugabanninta na yanzu suna kalubalantar ikon mallakar yankin kasar Sin, da gaskiyar tarihin yadda aka kawo karshen yakin duniya na biyu, da kuma tsarin kasa da kasa da aka amince da shi bayan yakin.

Wang Yi ya yi nuni da cewa, “Dole ne mu ci gaba da taka-tsantsan da sa-ido kan sake farfado da karfin soja na kasar Japan.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *