’Yan bindiga sun yi garkuwa da mata 8 a Sakkwato

[ad_1]



Wasu gungun ’yan bindiga sun sake kai hari ƙauyen Rarah da ke Ƙaramar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato, inda suka yi garkuwa da mata takwas, ciki har da mata masu juna biyu da mai shayarwa a yayin harin.

Majiyoyi daga ƙauyen da suka nemi a sakaya sunansu sun shaida wa wakilinmu cewa, maharan sun afka ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:00 na safe a ranar Laraba, inda suka kwashe kusan sa’a guda suna cin karen su ba babbaka kafin su tafi da mutanen zuwa inda ba a sani ba.

Sai dai, an sako ɗaya daga cikin matan jim kaɗan bayan sun bar ƙauyen.

Wani ɗan uwan waɗanda aka sace ya bayyana cewa al’ummar ƙauyen na fuskantar hare-haren akai-akai a cikin ’yan makonnin nan.

Ya yi zargin cewa, kimanin makonni biyar da suka gabata, ’yan bindiga da dama sun mamaye ƙauyen, inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 18, har da jariri ɗan wata biyu.

A cewarsa: “Mutane 12 daga cikin waɗanda aka sace mata ne, waɗanda wasun su ma masu juna biyu ne, tare da maza biyar da kuma ƙananan yara.”

Majiyar ta ƙara da cewa, maharan sun tuntuɓi ’yan uwan waɗanda aka sace inda suka buƙaci Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa, ya kuma ƙara da cewa, yawancin iyalai da lamarin ya shafa matalauta ne da ke fafutukar neman abincin yau da kullum.

“Har yanzu mutanen da aka sace fiye da makonni biyar da suka gabata suna hannunsu. ’Yan bindigar sun dage cewa sai an biya miliyan 20 kafin su sake su. Wasu daga cikin iyayen waɗanda abun ya shafa ma ba su da halin samun abinci mai kyau,” in ji shi.

Mazaunin ƙauyen ya kuma ba da labarin yadda aka kashe mahaifinsa duk da biyan kuɗin fansa har miliyan, yana zargin cewa ba a ba iyalinsa damar ganin gawarsa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *