Gwamna Fintiri ya fice daga PDP ya koma APC

[ad_1]



Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a ƙarshe ya fice daga Jam’iyyar PDP inda ya koma jam’iyyar APC mai mulki a matakin ƙasa.

Wannan sauyin sheƙa na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Bathiya Wesley, ya yi murabus daga Jam’iyyar PDP tare da wasu mambobin majalisar su 13.

Aminiya ta ruwaito cewa Fintiri ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar APC ne a mazaɓar K/Wuro Ngayandi da ke ƙaramar hukumar Madagali ta jihar, a ranar Juma’a.

Kafin wannan sauyin sheƙa, Fintiri ya kasance yana gudanar da jerin tarurruka da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC.

A ranar Laraba, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya jagoranci wasu manyan jami’an jam’iyyar na yankin zuwa wata ganawa da Fintiri a babban birnin Jihar da ke Yola.

“Wannan zama ya nuna ƙudurinmu na yin tattaunawa, haɗin kai, da kuma ci gaban Jihar Adamawa baki ɗaya. Ya zama dama ta tattauna muhimman batutuwan ci gaba da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa domin amfanin jama’a. Shugabanci da haɗin kai su ne ginshiƙin gina Adamawa mai zaman lafiya, ƙarko, da wadata,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci taron a shafukan sada zumunta.

Cikakken rahoton na nan tafe


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *