Babu Lokacin Da Aka Fi Bukatar Shawarar GGI Ta Shugaba Xi A Duniya Kamar Yanzu
[ad_1]
Tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a duniya sun kara tsananta kwarai da gaske tun bayan kaddamar da hare-haren kawancen Amurka da Isra’ila a kan kasar Iran da kuma zafafan martanin da Iran take mayarwa. Tun bayan dawowar shugaba Donald Trump na Amurka karagar mulki a farkon shekarar 2025, duniya take fuskantar wasu ire-iren sauye-sauye da masana ke cewa ba a taba ganin irinsu ba tun bayan yakin duniya na biyu.
Tsarin mabambantan bangarori da kasashen duniya suka shimfida kuma suka yi mubaya’a a kai a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a duniya na fuskantar barazanar wargajewa, sakamakon lullubin birin da aka yi wa babakeren Amurka da sunan shirin “sake mayar da Amurka gawurtacciya, watau MAGA.”
Tun kafin shiga wannan hali a duniya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya mai lakabin GGI yayin gudanar da taron kungiyar hadin gwiwar kasashe ta Shanghai (SCO) a shekarar 2025, da nufin kyautata yadda ake tafiyar da al’amuran harkokin kasa da kasa, ta yadda za su dace da zamani da kuma nuna gaskiya da adalci. Wannan ba karamin hangen nesa ba ne, domin a halin yanzu, duk kalubalen da ake fargabar aukuwarsu suna kara bayyana daya-bayan-daya kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a kwanan nan.
Babban abin da aka fi tsoro shi ne rugujewar tsarin kasa da kasa a karkashin inuwar MDD, domin hakan zai mayar da duniya zamanin bakin duhun zalunci da mulkin mallaka ta yadda kasashe masu karfi za su ci karensu ba babbaka a kan kananan kasashe, sannan daga bisani su juya kan junansu. Shugaba Xi ya taba bayyana cewa, bai kamata a mayar da muhallin rayuwar bil’adama ya zamo irin na namun daji ba wanda mai karfi zai buge mara karfi ya cinye, kuma an kama hanyar hakan tun daga lokacin da Amurka ta tura sojojinta suka shiga har cikin gidan kasar Venezuela suka sace shugaban kasar sukutum tare da ingiza keyarsa zuwa kurkukunta.
Dabi’un Amurka suna kara rura wutar rashin tabbas a fagen kasa da kasa, inda yanzu haka manyan kawayenta ciki har da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) suka fara debe tsammani da ita da kuma tunanin rage dogaro da tsarin mabambantan bangarori wajen fuskantar barazanar tsaro kamar yadda shugabar hukumar EU, Ursula von der Leyen ta bayyana kwanan nan. Shi ma shugaba Faransa ya fito fili ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da kera makaman nukiliya, kuma ba za ta fada wa duniya adadinsu ba.
Don haka, bisa la’akari da yadda abubuwa ke kara ta’azzara, babu lokacin da aka fi bukatar gaggauta amfani da shawarar GGI ta shugaba Xi kamar wannan lokaci domin sake daidaita tsarin kasa da kasa da zai yi wa kowane bangare adalci, lamarin da ke bukatar goyon baya da gudunmawar al’ummomin kasa da kasa. Kumma tabbas za a iya cimma hakan, kamar yadda gaggan kawayen Amurka suka kware mata baya ta hanyar kin shiga da ba da sansanoninsu don kai hare-hare na fitinar da ta tayar ita da Isra’ila a kan Iran. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link