Gadar Da Sin Ta Gina Ta Inganta Yawon Bude Ido A Tsibirin Kasar Mozambique
[ad_1]
Shugaban Mozambique Daniel Francisco Chapo, ya halarci bikin kaddamar da wata gada da aka gina cikin ruwa a tsibirin Inhaca dake gabar ruwa ta Maputo a jiya Juma’a. Kamfanin gine ginen tituna da gadoji na kasar Sin, CRBC ne ya gudanar da aikin gadar.
Tsibirin Inhaca mai tazarar kilomita 30 daga Maputo babban birnin kasar, na da kimanin mazauna 6,000 kuma ya yi fice ne saboda albarkatun yawon bude ido. A baya, ruwa mara zurfi dake kewayen tsibirin ya hana jiragen ruwan jigilar fasinja isa bakin tsibirin kai tsaye, lamarin dake tilasta wa fasinjoji komawa kananan kwale-kwale.
Sabuwar gadar mai tsayin kilomita 1.3, na ba jiragen ruwan fasinjoji damar tsayawa a bakin tsibirin karkashin ko wane yanayi. Kuma yanzu, masu ziyara na iya kai wa tsibirin kai tsaye ta hanyar amfani da gadar, lamarin da ya kyautata tsaro da ingancin sufurin fasinjoji. (Mai fassara: FMM)
[ad_2]
Source link