Yanzu Maza Sun Waye Ba Sa Son Bayar Da Ramadan Basket

[ad_1]

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban, waɗanda suka shafi al’umma.

Tsokacinmu na yau, zai yi duba ne game da Ramadan Baske, wanda masoya ke kai wa juna. Shin har yanzu wannan al’ada tana nan ko kuwa ta sauya zani?

Dalilin haka ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; “Ko wacce wainar ake toyawa game da Ramadan Basket a wannan shekarar? Ya batun tsadar kaya wajen kawo barazana ga masu haɗa Ramadan Basket? Wacce shawara ya kamata a bai wa matasa masu ƙoƙarin haɗa Ramadan Basket ko kayan toshi, musamman masoyan da suke rabuwa da juna saboda rashin Ramadan Basket?

  • An Fara Bincike Bayan Mutuwar Mutum Huɗu A Turmutsutsun Karɓar Tallafin Ramadan A Katsina
  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 18

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Ƙaura-Namoda, Jihar Zamfara:

Ramadan Basket, a wannan shekarar maza da yawa sun jingine wannan al’adar. Duk da wasu masu ƙwarin zuciya da ƙarfin kyautatawa, sun yi wa ‘yan matansu. Amma kashi bakwai cikin goma na masu yi, sun jingine. Tabbss tsadar kaya ya taka muhimmiyar rawa, ta wani gefen kuma kiranyen da wasu malamai ke yi wa samarin, a kan cewa babu dole ba sai sun yi ba.

Hakan ya gurgunta zuciyoyin masu fafutukar son burge waɗanda suke so a irin wannan fuskar. Wasu kuma da man can hannun ‘yan dambe gare su, sai suka samu hanyar fakewa, domin doje wa Ramadan Basket. Shawarata ga matasa masu ƙoƙarin haɗa Ramadan Baske, kada su daina su yi iya ƙarfinsu, saboda tukuicin so, kyauta ne. A duk lokacin da suka kyautata, ana jin daɗi, sannan kuma soyayya tana ƙara danƙo.

Har ila yau, matan da suke ƙwallafa rai a kan don an yi wa wata, su ma dole sai an yi musu, idan kuma ba a yi musu ba su rabu da mai son su; sun jahilci zaman gaskiya da amana. Idan akwai ƙauna ta domin Allah, wannan dalilin bai kai matsayin da zai raba soyayya ba.

Sunana Fatima Nura Kila, Jihar Jigawa:

Batun Ramadan Basket, kusan yanzu gaskiya ba a fiya yin sa ba, duba da yadda kayan masarufi, musamman na shago yake tsada, sannnan babu kuɗi a hannun samari. Tabbas tsadar kaya ya yi yawa, yayin da a da mutum dubu goma ta isa a haɗa Ramadan Basket, amma yanzu sai a haɗa na dubu hamsin, kuma ba wani kayan a zo a gani ba ne.

Har kullum, matuƙar kina son mutum, ki so shi saboda Allah, domin idan wata rana akwai, wata ranar babu, idan babu sai ki tuno alhairansa a gare ki.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, a Jihar Kano:

Gaskiya ban ji ana maganar Ramadan Baske ba a namu yankin, duk da kayan ba ya tsada kamar shekarun baya, amma kuma kuɗin ne babu sosai a hannun mutane. Ai ba lefin tsadar kaya ba ne kaɗai, a samu a yi ɗinkin sallah da kuma abin da za a ci a wannan azumin shi ne ya fi a kan Ramadan basket. Shawarata a gare su ita ce, kawai su sadaukar da kuɗin wajen ɗinka wa marayun unguwarsu kayan sallah ko kuma su ciyar da mabuƙata a cikin wannan watan na Ramadan, zai fi musu. Allah kasa mu dace, amin.

Sunana Khadija Auwal Ahmad Ƙoki, A Jihar Kano:

Eh to, Ramadan basket, ana nan ana yi; wasu tuni sun riga sun yi, wasu kuma sai nan gaba. Gaskiya A’a, ai kayan ba kamar da ba, Alhmadulillah, yanzu kuma babu abin da ya sauya na game da masu haɗa Ramadan basket ɗin. Gaskiya shawarar da zan bayar ita ce, idan aka samu rabuwa saboda abin duniya, to wannan soyayyar daman ba ta Allah ba ce, koda-yaushe zai iya rabuwa da ke, don haka idan ya dawo ta yi nazari sosai a kansa.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, Daga Jos, Jihar Filato:

Ra’ayina game da batun Ramadan Basket zan iya cewa, ai tuni ya zama tsohon ya yi. Koda-yake, ya zama kamar wata al’ada, amma har yanzu akwai masu yin hidimar Ramadan Basket, domin nuna wa wacce suke so tsantsar ƙauna tare da ɗaga darajarta a tsakanin ƙawayenta da ‘yan’uwa.

Sai dai, gaskiya yanzu ba kamar a shekarun baya ba, musamman a manyan birane, hidimar Ramadan Basket ta zama tsohuwar al’ada, saboda sauyin yanayin zamantakewa, tattalin arziƙi da ci gaban rayuwa. Samari sun fi mayar da hankali wajen saya wa ‘yan matansu wayoyi masu tsada da ɗinkin kayan sallah, ko dai wata kyauta ta musamman, ba lallai cikin tsarin baya na Ramadan Basket ba. Ramadan Basket, abu ne da yake ƙara danƙon soyayya a tsakanin masoya, yanayin rayuwa yanzu ya sa tilas a yi haƙuri da abin da ya samu, a tafiyar da rayuwa a yadda ta zo. Kadaran-kadahan!

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, Ƙaramar Hukumar Dala, Jihar Kano:

Ramadan basket, wani nau’in farantawa ne, kuma al’ada ce mai kyau da ta daɗe tana gudana tsakanin masoya, tun shekaru aru-aru. A lokutan baya, wannan al’ada ta fi tasiri duk da cewa, a lokacin ba wasu kaya ba ne masu yawa ake yi ko kuma ƙayyadewa.

Daidai ƙarfin saurayi zai yi wa budurwarsa abin da zai faranta mata rai tare da sanya mata farin ciki, sannan ya fitar da ita kunya. Idan bai yi mata ba, ba ta nuna damuwa ko kuma ta nemi su ɓata. To sai dai, a wannan zamanin al’adar ta sauya sosai, abin ya zama wani iri daban. ‘Yan mata, su kan ɗora buri sosai a kan Ramadan basket, wanda hakan ke razana wasu daga cikin samarin har ta kai ga an ɓata.

Bayan haka, akwai tasirin tsadar kayayyaki a irin burin ‘yan mata na wannan zamani, ba sa kallon abin da ake kawowa a matsayin kyautatawa da kulawa. Sun fi mayar da hankali a kan yawan abin da za a kawo musu.

Don haka, shawarata ga matasa ita ce, su yi ƙoƙari daidai gwargwadon ƙarfinsu su yi abin da zai faranta wa ‘yan matansu rai, kada ƙarancin abin da zai yi ya hana shi yi, lallai ya yi ko da babu yawa. Su ma ‘yan matan su gane, idan samarinsu ba su yi musu Ramadan basket ba, ko kuma suka yi kaɗan, to su karɓa su yi godiya su nuna farincikinsu.

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

Ramadan Basket, wani alhairi ne wanda masoya suka sanya masa wannan suna na Ramadan Basket, a nawa tunanin, bai zama dole sai an yi wani abu ba. Idan mutum ya kawo maka sai ka karɓa, idan bai kawo maka ba, ka haƙura, ba abu ne na takurawa ba.

A halin yanzu, ba za a iya cewa; akwai tsadar kaya da zai hana yin Ramadan Basket ba, musamman ga me niyya, yanzu an samu sauƙi sai dai a ce Alhamdulillah, a kan waccan shekarar.

Sunana Aisha T. Bello, Jihar Kaduna:

Yanzu gaskiya maza sun waye, ba sa son bayar da Ramadan Basket, amma duk da haka kuma akwai masu bayar wa. Eh, maza yanzu ba sa son ba da Ramadan Basket, saboda tsadar rayuwa, amma mata idan ba a ba su ba, wasu har rabuwa ake a kansa, gaskiya musamman wacce take tara samari, za ki ji tana wane na ji shiru batun Ramadan Basket ɗinsa, to gaskiya idan rowa ce, za mu rabu da shi ba na yi, haka wasu matan suke yi.

Saboda haka, shawarata a nan ga masu Ramadan Basket, musamman mata waɗanda suka mayar shi dole, Ramadan Basket ba dole ba ne, su yi haƙuri rayuwa ce ta canja, yadda rayuwar take a da, yanzu ba haka take ba. Ramadan Basket ba dole ba ne. Don haka, mata don Allah mu yi haƙuri, Allah ya ba mu dacewa, amin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *