Darussa Daga Ramadan Na 11: Sauƙi Da Sassauci A Shari’a

[ad_1]

A cikin watan Ramalana muna koyon sauƙaƙawa da sassautawa a cikin al’amuranmu na yau da kullum, matuƙar hakan ba zai kai zuwa ga saɓon Allah ba.

  • Darussa Daga Ramadan Na 10: Zumunci Da Tausayi
  • Darussa Daga Ramadan Na 9: Danne Fushi Da Nutsuwa A Ramalana

Ramalana, duk da cewa wata ne na ibada mai tsanani, amma a cikinsa ne Allah Ya bayyana mana cewa addinin Musulunci addini ne na sauƙi, ba na tsanani da takura ba. Allah Maɗaukaki Ya ce a cikin Suratul Baƙara aya ta (185): “Allah Yana nufin sauƙi a gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani a gare ku” Wannan aya ta zo ne a tsakiyar hukunce-hukuncen azumi, wadda ibada ce mai ɗauke da yunwa da ƙishirwa. Amma duk da haka, Allah Ya bayar da rangwame ga marasa lafiya, da matafiyi, da waɗanda ba za su iya ba.

Wannan yana nuna cewa shari’a ba ta zo domin wahalar da bawa ba, sai dai domin gyara shi da ɗora shi a bisa turbar rahama. Haka kuma, Manzon Allah (SAW) ya kasance abin koyi a wannan fanni. Ya zo a cikin Sahihul Bukhari cewa: “Ba a taɓa ba wa Manzon Allah zaɓi a tsakanin al’amura biyu ba, face ya zaɓi mafi sauƙi a cikinsu, matuƙar ba saɓo ba ne. Idan kuwa saɓo ne, to, shi ne ya fi kowa guje masa”

Wannan hadisi yana koya mana daidaito. Sauƙi a Musulunci ba sakaci ba ne, kuma tsanani ba alamar tsoron Allah ba ne. Abin da ake so shi ne bin umarni cikin hikima da sassauci, tare da nisantar abin da Allah Ya hana.

Ramalana yana koya mana cewa; addini ba ya hana sauƙi idan yana cikin halal. Sassauci yana daga cikin halayen Annabi (SAW).

Tsanani da ƙuntatawa kai ko mutane ba su ne ma’aunin ibada ba. A wasu lokuta mutum yana ɗaukar tsanani a matsayin ƙarfi a addini, alhali kuwa sauƙi da sassauci su ne mafi kusanci da sunnar Annabi (SAW) a gida, da wurin aiki, da cikin mu’amala da al’umma, idan muka riƙe wannan ka’ida, to, mu riƙa zaɓar abu mafi sauƙi muddin ba saɓo ba ne, yin haka zai sanya mu samu kwanciyar hankali da daidaito.

Sai dai a lura, sauƙi ba ya nufin wuce gona da iri ko sakaci. Idan al’amari ya kai ga saɓo, to mumini ya fi kowa nisantar sa. Wannan shi ne mizani na gaskiya, sassauci cikin abin da yake halal, tsayuwa daram a kan nisantar haram.

Idan muka fahimci wannan darasi daga Ramalana, to rayuwarmu za ta zama mai sauƙi, zuciyarmu za ta samu natsuwa, kuma hulɗarmu da mutane za ta inganta.

Allah Ya sa mu kasance masu fahimtar sauƙin addini, masu bin sunnar Annabi (SAW) cikin hikima, Ya kuma tsare mu daga tsanani da sakaci. Amin.

Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *