2027: An matsa min kan yin takarar Sanata — Gwamna Sule

[ad_1]



Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce zai iya tsayawa takarar kujerar Sanata a shekarar 2027.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da mambobin majalisar zartarwa ta jihar suka kai masa, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamna, Dakta Emmanuel Akabe, a gidansa da ke Gudi, a Ƙaramar Hukumar Akwanga.

Gwamnan ya ce shugabanni da masu ruwa da tsaki da dama suna matsa masa lamba ya tsaya takarar kujerar Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa.

Saboda wannan matsin lamba, ya ce yana duba yiwuwar tsayawa takarar.

“Duba da irin matsin da shugabanninmu ke yi, ba na son su ji kamar ban mutunta su ba. Zan iya musu alƙawarin zan tsaya takara idan lokaci ya yi,” in ji shi.

Sule ya ce tun da farko yana da niyyar mara wa wani baya, amma daga baya ya sauya shawara bayan mutumin ya haɗa kai da wasu wajen roƙonsa da ya tsaya takara.

Ya ƙara da cewa har yanzu yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki, ciki har da sarakunan gargajiya da manyan ’yan siyasa daga yankin Nasarawa ta Arewa, kafin ya yanke hukunci na ƙarshe.

Gwamna Sule na wa’adinsa na biyu a mulki, kuma zai sauka bayan kammala wa’adin.

A jawabinsa, mataimakin gwamnan ya sake jaddada goyon bayan majalisar zartarwar jihar ga gwamnan, yana mai cewa za su ci gaba da mara masa baya har zuwa ƙarshen wa’adinsa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *