Wang Huning Ya Gana Da Wani Farfesan Jami’ar Harvard
[ad_1]
Shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin wato CPPCC a takaice, Wang Huning, ya gana da farfesan jami’ar Harvard Graham Allison, a jiya Jumma’a a nan birnin Beijing.
Yayin zantawarsu, Wang ya ce, Sin za ta ci gaba da fuskantar yawaitar sauye-sauyen yanayin kasa da kasa cike da tabbaci game da ci gaban kanta, a daidai gabar da a bana ta shiga shekarar farko ta aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 15.
Wang, ya jaddada cewa batun Taiwan na kan gaba, cikin manyan moriyar kasar Sin. Kuma kamata ya yi Sin da Amurka su inganta tattaunawa da tuntuba, su shawo kan sabaninsu yadda ya kamata, su fadada hadin gwiwa na hakika, kuma su samar da hanya ingantacciya ta tafiya tare, da ingiza samar da tabbaci da kyakkyawan karsashi cikin duniya.
A nasa bangare, farfesa Allison cewa ya yi a halin da ake ciki, an riga an yi matukar illata yanayin zama lafiya da odar duniya, kuma yana da matukar muhimmanci Amurka da Sin su zakulo hanya madaidaiciya ta yin tafiya tare.
Allison, ya kara da cewa, fatan shi ne Amurka da Sin za su shawo kan batutuwa yadda ya kamata, ciki har da batun Taiwan, kana su tabbatar da samar da daidaitaccen ci gaban dangantakarsu, kasancewar hakan ya yi daidai da muradun dukkanin kasashen duniya. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link