Sin Ta Karrama Matan Da Suka Zamo Ababen Koyi Gabanin Bikin Ranar Mata Ta Duniya
[ad_1]
Babbar kungiyar mata ta kasar Sin, watau ACWF a takaice, ta gudanar da wani taro a birnin Beijing jiya Litinin, domin bikin ranar mata ta duniya wadda aka saba gudanarwa a duk ranar 8 ga watan Maris, tare da karrama fitattun mata da suka zamo ababen koyi a fadin kasar.
Jimillar mutane 607, da kungiyoyi 400 da wuraren aiki 600 ne suka karbi lambobin yabo a wurin taron.
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, wadda ita ce shugabar kungiyar ACWF, ta yi jawabi a wajen bikin, inda ta mika gaisuwa ga mata a sassa daban-daban da na kabilu mabambanta, tare da taya wadanda aka karrama murnar samun lambar yabo.
Shen ta yi kira ga mata a duk fadin kasar Sin da su ba da gudummawa sosai ga ci gaban kasar a babban mataki na inganci, da yin aiki tukuru don ciyar da shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15 (2026-2030) gaba.
Ta kuma ba su kwarin gwiwa a kan su tsunduma cikin harkokin jagoranci na duniya, da bayyana hikimar kasar Sin wajen karfafa manufofin ci gaban mata a duniya da kuma zurfafa wayewar kan dan’adam. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link