Ramadan: Akpabio Ya Bukaci Musulmai Su Yi Addu’a Don Zaman Lafiyar Kasa
Yayin da aka fara gudanar da watan azumin Ramadan, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a don zaman lafiya a Nijeriya da duniya baki daya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ga ‘yan jarida a jiya a Abuja ta bakin mashawarcin sa na musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Sanarwa, Hon. Eseme Eyiboh, Akpabio ya bukaci mabiya addinin Musulunci da su rungumi ma’anar ruhaniya ta Ramadan ta hanyar nuna tausayi, karfafa fahimtar juna, da inganta hadin kai.
- Ramadan: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci Ga Limamai 40 A Zamfara
- An Kama Wadanda Ake Zargi Masu Garkuwa Ne 12 Da Wasu 83 A Jihar Ondo
“Yayin da al’ummar Musulmi ke shirin gudanar da ibada a watan azumin Ramadan, ina mika gaisuwa mafi dumi da fatan alheri ga dukkan Musulmai a Nijeriya da duniya baki daya,” in ji sakon.
“Ina rokon al’umma Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci mai tsarki a matsayin dama ta tunani na ruhaniya, kyautata kai, da sabunta imani. Bari wannan lokaci ya karfafa bangaskiyarku, ya karfafa ayyukan alheri, kuma ya inganta zaman lafiya da fahimtar juna.
“Allah ya kawo wannan Ramadan da zaman lafiya, arziki, da albarka ga iyalanku da kuma Nijeriya baki daya. Ina muku fatan Ramadan mai cike da salama da ruhaniya, kuma Allah ya karBi azuminku, addu’o’inku, da ayyukan alherinku. ‘Happy Ramadan’ ga dukkan Musulmai, kuma Allah ya albarkace mu duka.”