Sin Da Jamus Suna Kokarin Hada Gwiwarsu Don Samarwa Duniya Tabbaci
[ad_1]
Kwanan nan, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban gwamnatin kasar Jamus Friedrich Merz a birnin Beijing, ya nuna cewa, kamata ya yi kasashensu biyu su karfafa tattaunawa bisa manyan tsare-tsare da kara amincewa da juna a siyasance, musamman a yayin da duniya ke fuskantar hali mai sarkakiya da sauye-sauye, ta yadda karfin dangantakar kasashen biyu zai kai ga samarwa duk fadin duniya tabbaci. Wannan furucin ba wai kawai ya nuna alkibla ga dangantakar Sin da Jamus a sabon zamani ba, har ma ya ba da tabbaci ga tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, duba da kalubalen da ake fuskanta wajen tsarin jagorancin duniya.
A halin yanzu, ana fuskantar kunno kan ra’ayin bangaranci da nuna fin karfi a duniya, a yayin da kuma ake fuskantar kalubale ta fannin gudanar da harkokin kasa da kasa bisa tsarin dokokin duniya. Shugaba Xi ya sha jaddada cewa, ya kamata a kiyaye tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, da kuma kiyaye odar kasa da kasa bisa tushen tsarin dokokin duniya. A watan Satumba na shekara ta 2025, Xi ya gabatar da shawarar inganta tsarin shugabancin duniya, inda ya yi kira da a kiyaye daidaito tsakanin kasa da kasa wajen ikon mulkin kansu, da gudanar da harkokin duniya bisa tsarin dokokin kasa da kasa, da nacewa ga ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori a duniya, kana da sanya moriyar jama’a a gaba da komai. Wannan shawara ta dace da yanayin zamani, har ma ta samu goyon bayan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 150.
Ganawar shugabannin Sin da Jamus a wannan karo, ita ce misali mai kyau na tabbatar da ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori a duniya. A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya nuna cewa, ya kamata Sin da Jamus su mutunta matsayin MDD, da farfado da rawar jagoranci da MDD ke takawa, su kuma zama masu jagora a bangaren kiyaye ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori a duniya, da aiwatar da dokokin kasa da kasa, da kare ciniki cikin ‘yanci. Kuma wannan ra’ayi ya samu amincewa daga bangaren Jamus.
Hadin gwiwar kasuwanci da tattalin arzikin kasashen biyu shi ne muhimmin bangaren dangantakar Sin da Jamus, kuma muhimmancinsa ya wuce huldar kasashen biyu. Shugaba Xi a yayin ganawar, ya nuna cewa, bangarorin Sin da Jamus ya kamata su zama abokan hadin gwiwa na kirkire-kirkire da ke bude kofa ga juna da cin moriyar juna, kuma ya kamata bangarorin biyu su karfafa mu’ammala da juna ta fannin manufofin raya kansu, su inganta tattaunawa da hadin gwiwa a fagen fasahohin zamani kamar su fasahar AI da sauransu. Hakan ya samar da alkibla wajen zurfafa hadin gwiwar kasuwanci da tattalin arziki a tsakaninsu, kuma ya karawa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa da kuzari.
Dakatar da yaki da inganta zaman lafiya shi ne abin da aka sa gaba wajen inganta tsarin shugabancin duniya. Idan babu zaman lafiya, ta yaya za a yi magana game da tsarin shugabancin duniya? Bangarorin Sin da Jamus a cikin hadaddiyar sanarwarsu, sun ambaci batun Ukraine, inda suka nuna goyon bayan kokarin da ake yi na tsagaita bude wuta da kuma cimma zaman lafiya mai dorewa bisa kundin tsarin MDD.
Daga fitar da hadaddiyar sanarwa don kare ikon MDD, zuwa zurfafa hadin gwiwar kasuwanci don samar da sabon karfi ga tattalin arzikin duniya, Sin da Jamus sun sauke nauyin dake wuyan manyan kasashe bisa ainihin matakan da suke dauka. Kasashen biyu sun zabi tattaunawa maimakon warewa, hadin gwiwa maimakon katse huldar tattalin arziki, cudanyar mabambantan bangarori maimakon ra’ayin bangaranci, yayin da ake fuskantar hadarin rarrabuwar kawuna da adawa da juna, wannan shi ne tabbacin da duniya mai fuskantar rashin hankali take matukar bukata, kuma shi ne hakikanan matakan da ake dauka wajen tabbatar da tsarin shugabancin duniya. (Marubuci: MINA)
[ad_2]
Source link