Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959. (2)
…ci gaba daga makon da ya gabata.
Wannan labarin da Sarkin Zazzau Jafar Dan Isiyaku ya rubuta da kan shi ci gaba ne daga wanda aka fara wallafawa makon da ya gabata.
Muka shiga garin muka tarar ba kowa, duk sun gudu mazan su da matan su. Na kira Sarakunan su da basu cikin tawayen, na gaya musu su lallashi mutanen su, su dawo, babu komai. Washegari ni kuwa na y tafiya zuwa Mabushi. A can na samu labarin sun dawo sai shi Gankwan da ya harbi Sarkin fada na shine ba’a gani ba. Na aika ga Sarkin Zazzau Dalhatu da abinda ya faru duka, yace in kara matsawa kan neman Gankwan. Amma Ina? Ai har yau ba’a same shi ba, kamar an yi biyan bashi da shi. Sarkin fada na kwanan sa wajen Arba’in a Mabushi yana jinyar dafin kibiyar nan da Gankwan ya harbe shi.
Kai mutanen Zangon Katab a lokacin suna da wuyar sha’ani wajen al’amarin Haraji! Dubi wata shekara kuma da ni da wani Joji muna kama Awakin wadanda basu biya Haraji ba a Zankuwa, ba sai muka kama na wani wanda ya biya ba? sai gashi faram faram da matar sa suka zo suka durkusa suka ce mana “Wadannan Awaki namu ne, mu kuwa mun biya Haraji” Joji yace “To mu dai mun kama Awaki. Watau Makwafcin ka ya biya ke nan, in ya samu kudi sai ya biya ka.”
Da suka koma gida sai matar sa ta shiga zuga mijin tana cewa “Allah wadan ka! Ashe dai kai ba Namiji bane? yaya don tsoron Sarauta zamu yarda a kwace mana Awaki? Ina ruwan mu da Makwafcin mu da zamu biya masa Haraji? Kai in baka dauki kwari da baka ka tara da Baturen nan ba, ina sa wuta in kone su, in kuma rabu da kai.” Daga nan sai maigida ya dauki Kwari da baka ya tanka, ‘ya’yan sa kuma kowa ya dauko tasa, suka nufo wajen mu za su tada Jihadi. Da na hango shi sai na daka masa tsawa sai ya yada Baka ya zo ya fadi gabanmu yana haki. Na lallashe shi, na bashi magana sa’an nan ya koma. Ka ji tashin hankulan da na hadu dasu lokacin ina Hakimcin Zangon Katab.
Na samu wannan Sarautar zamanin Sarkin Zazzau Aliyu ne, bayan shi aka nada Dalhatu. Daga nan sai Sarkin Zazzau Ibrahim ya kama Sarauta, shi kuma ranar 31/1/1937 ya rasu. Allah ya jikan su Amin. Bayan rasuwar Sarkin Zazzau Ibrahim, ina Hakimci a Zangon Katab sai ga waya ana nema na a Zariya, don Gwamna da manyan mashawartan Zazzau sun yarda in zama Sarki a shekarar 1936.