Sabon kocin Chelsea Rosenior ya soma jan ragama da ƙafar dama

[ad_1]



Sabon kocin Chelsea, Liam Rosenior, ya soma jan ragamar ƙungiyar da ƙafar dama wadda ya jagoranta wajen doke Charlton da ci 5-1 a wasan zagaye na uku na gasar FA Cup da aka buga ranar Asabar.

Chelsea ta fara zura ƙwallo ne daf da tafiya hutun rabin farko ta hannun Jorrel Hato, wadda ita ce ƙwallonsa ta farko a ƙungiyar, kafin Tosin Adarabioyo ya ƙara ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Ko da yake Miles Leaburn ya rage wa Charlton ƙwallon ɗaya, amma Marc Guiu, Pedro Neto da Enzo Fernandez sun ƙara yawan ƙwallayen, lamarin da ya tabbatar wa Rosenior nasara a wasan farko.

Rosenior, mai shekaru 41, wanda aka ɗauko daga Strasbourg domin maye gurbin Enzo Maresca, ya kawo ƙarshen jerin wasanni biyar da Chelsea ta yi ba tare da nasara ba. Ya kuma cika alƙawarin da ya yi na fara aiki “da ƙafar dama”.

Duk da ana ce-ce-ku-ce kan yarjejeniyar aka ɗauke shi aiki, Rosenior ya nuna ƙwarewa ta hanyar yin sauye-sauye takwas a tawagarsa, har ma ya bar Cole Palmer a benci.

Haka kuma, Rosenior ya ci gaba da amfani da tsarin tsaron ’yan baya uku kamar yadda ya saba a Strasbourg.

Chelsea ce dai ta riƙe akalar wasan gaba ɗaya, inda ta nuna ƙwazo da dagewa har zuwa mintuna na ƙarshe, lokacin da Neto ya ci ƙwallo ta huɗu, sannan Enzo Fernandez ya rufe wasan da bugun fanareti a mintin ƙarshe.

Ƙalubale na gaba da Chelsea za ta fuskanta na farko ƙarƙashin Rosenior shi ne wasan da za ta karɓi baƙuncin Arsenal a wasan kusa da na ƙarshe na gasar League Cup.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *