Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na biyar na gasar cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) da ke ci gaba da gudana a kakar nan.

Wasan da za a buga a filin Stamford Bridge, yana zuwa ne bayan da ’yan wasan Barcelona suka ƙauracewa atisayi a bainar jama’a domin ɓoye salon horon su.

Chelsea da Barcelona sun haɗu sau 14 a gasar Zakarun Turai, inda kowacce ƙungiyar ta yi nasara huɗu, sannan aka yi kunnen doki shida.

Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyoyin za su kara tun kakar 2017/18 a zagayen ’yan 16, lokacin da Barcelona ta yi nasarar tsallakawa zagaye na gaba, bayan cin jimilla 4–1 a waje da gida — wanda aka tashi 1–1 a Stamford Bridge da kuma nasarar 3–0 a Sifaniya.

Chelsea ta sha kashi sau ɗaya ne kawai daga wasanninta bakwai da ta yi a gida a gasar Zakarun Turai da Barcelona — inda ta yi nasara huɗu tare da tashi kunnen doki biyu a Stamford Bridge.

Haka kuma, Chelsea ta  cin wasa biyu a fafatawa 61 baya a gasar Zakarun Turai a gida, sannan ba ta yi rashin nasara ba a fafatawa 16, wadda ta ci 12 da canjaras huɗu — tun bayan doke ta 1-0 da Valencia a Satumbar 2019.

A gefe guda, Barcelona ta yi rashin nasara uku ne kacal daga wasa 20 a Champions League da ta fuskanci wata ƙungiyar Ingila, bayan cin 13 da canjaras huɗu da kuma rashin nasara ɗaya daga fafatawa 11, baya ga samun nasara a karawa takwas da canjaras biyu daga ciki.

Lamine Yamal, wanda zai cika shekara 18 da kwana 135 ranar Talata, ya riga ya zura ƙwallo bakwai a Champions League kafin cikarsa shekara 19.

Yana buƙatar ƙarin uku domin ya yi daidai da tarihin Kylian Mbappé a wannan rukuni.

Barcelona ta zura ƙwallo 96 a raga cikin wasanninta 20 na baya-bayan nan a Champions League.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *