Manchester United za ta ɗauki golan Antwerp, Senne Lammens
[ad_1]
Manchester United ta amince za ta ɗauki golan tawagar Belgium, Senne Lammens daga Royal Antwerp kan fam miliyan 18.1 har da karin tsarabe-tsarabe.
Sasashen wasanni na BBC ya ruwaito cewa hakan ya kawo karshen zawarcin golan Aston Villa, Emiliano Martinez da ta yi.
Lammens, mai shekara 23, zai saka hannu a ƙungiyar Old Trafford kan yarjejeniyar kaka biyar.
United na fatan ɗinke ɓarakar gurbin mai tsaron raga, bayan da Altay Bayindir ke kuskure a wasannin Firimiya, yayin da ake zargin Andre Onana da sakacin da ya janyo aka fitar da United a Carabao Cup a hannun Grimsby.
Lammens ya koma Antwerp a matakin mara ƙunshin yarjejeniya daga Club Brugge a 2023, wanda ya tsare raga karo 64 a Antwerp da lashe Belgian Super Cup a 2023.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link