Ɗan ƙasar Ghana Daniel Laryea zai yi alƙalancin wasan Najeriya da Morocco

[ad_1]



Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta sanar da jami’an da za su jagoranci wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Najeriya da Morocco wanda za a fafata a gobe Laraba.

Hukumar ta ayyana Daniel Nii Ayi Laryea ɗan ƙasar Ghana a matsayin babban alƙalin wasan da zai jagoranci wasan a tsakiyar fili.

Sauran jami’an da za su jagoranci alƙalancin wasan, sun haɗa da Zakhele Thusi Granville Siwela daga Afirka ta Kudu, Souru Phatsoane daga Lesotho, Arsenio Chadreque Maringule daga Mozambique, sai kuma Samuel Uwikunda daga Rwanda.

Daniel Laryea gogaggen alƙalin wasa ne, kuma kwanan nan ya jagorancin na’urar da ke taimakon alƙalan wasa VAR a wasan Morocco da Kamaru.

Haka kuma, shi ne ya yi alƙalancin wasan Algeria da Burkina Faso a matakin rukuni.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *