Ba na cikin sahun waɗanda za su maye gurbin Amorim a United — Howe

[ad_1]



Eddie Howe ya bayyana cewa ya raja’a kacokam wajen ci gaba da aikin horas da ’yan wasan ƙungiyar Newcastle, inda ya musanta jita-jitar da ke alaƙanta shi da karɓar aikin horas da Manchester United.

Howe ya faɗi hakan ne a ranar Talata, yana mai cewa yana da yaƙini ɗari bisa ɗari wajen ci gaba da aikinsa a St James’ Park.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Manchester United ta kori kocinta, Ruben Amorim, wanda suka raba gari a ranar Litinin, bayan shafe watanni 14 yana jagorantar ƙungiyar ta Old Trafford.

An kori Amorim ne bayan wata hira mai zafi da ya yi bayan wasan da United ta tashi 1-1 da Leeds United.

Bayan sallamar Amorim, an fara raɗe-raɗin cewa Howe na daga cikin waɗanda ka iya maye gurbinsa a matsayin sabon kocin Manchester United na dindindin.

Haka kuma, a bayan nan an alaƙanta Howe da aikin horas da Chelsea, bayan rabuwar ƙungiyar da kocinta Enzo Maresca a makon da ya gabata.

Tuni dai Chelsea ta riga da naɗa tsohon kocin Strasbourg, Liam Rosenior, a matsayin sabon kocinta.

“Ina farin ciki a Newcastle”

Howe mai shekaru 48, ya shaida wa ‘yan jarida cewa babu wani abu da zai ja hankalinsa ya bar Newcastle a halin yanzu.

Ya ce: “A’a, ba a wannan lokaci ba. Abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne samun farin ciki a aikin da nake yi, da jin daɗi a rawar da nake takawa, da kuma alaƙar da ke tsakanina da mutanen da nake aiki da su.

“Ba lallai ne waɗannan abubuwa su kasance masu kyau koyaushe ba, domin abubuwa kan sauya a kowace ƙungiyar ƙwallo. Amma a halin yanzu, ina matuƙar farin ciki.”

Tarihinsa a Newcastle

A halin yanzu dai wannan ita ce kaka ta biyar da Howe ke jan ragamar Newcastle United, inda a bara, ya jagoranci ƙungiyar wajen lashe babban kofi na farko cikin shekaru 56, abin da ya sanya sunansa a tarihin kulob ɗin.

A yanzu haka, Newcastle na matsayi na tara a teburin Firimiyar Ingila, da tazarar maki biyar kacal tsakaninta da gurbin shiga sahun masu samun tikitin zuwa gasar Champions League.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *