CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana.
A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana.
Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe a FIFA Club World Cup da Chelsea ta lashe a Amurka.
Shi kuwa Mohammed Salah ya taka rawar gani a Liverpool a kakar da ta wuce da lashe Premier League, kuma shi ne kan gaba a zazzaga kwallaye mai 29 da bayar da 18 aka zura a raga, hakan ya sa ya karbi kyautar takalmin zinare, wato Golden Boot.
Mohammed Salah dan ƙasar Masar mai shekara 33 na fatan karbar kyautar gwarzon Afirka karo na uku bayan 2017 da kuma 2018.
Shi kuwa dan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya, Victor Osimhen ya jagoranci Galatasaray ta dauki babban kofin tamaula na Turkiya da cin ƙwallo 26.
Osimhen ya taba zama gwarzon Afirka 2023 a lokacin da shi kuma Hakimi ya yi na biyu
To sai dai mai riƙe da kyautar a yanzu, wato Ademola Lookman na Nijeriya, bai kai bante ba a kakar nan sakamakon gaza taka rawar gani yadda ake buƙata.
Za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan ƙwallon ƙafa na Afirka na bana ranar Laraba a birnin Rabat na Morocco.