AFCON 2025: CAF ta ci Senegal da Maroko tarar sama da $1m
[ad_1]
Kwamitin Ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ya sanar da cin tarar kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Senegal da ta Maroko, tare da wasu ’yan wasa da jami’ansu sama da Dala miliyan daya.
Hukumar dai ta dauki matakin ne saboda takaddamar da ta faru a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Afrika ta 2025 a tsakanin kasashen biyu.
A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin CAF, hukumar ta ce an ɗauki matakan ne saboda karya dokokin ladabtarwa na hukumar, ciki har da tauye ka’idojin wasa, aminci da gaskiya, yayin wasan karshe da kuma bayan shi.
A bangaren Senegal, CAF ta dakatar da kocin ƙungiyar, Pape Bouna Thiaw, daga wasanni biyar na CAF saboda rashin ladabi da tauye mutuncin wasa, tare da cin shi tarar dalar Amurka 100,000.
Haka kuma, an dakatar da Iliman Cheikh Baroy Ndiaye da Ismaila Sarr daga wasanni biyu-biyu saboda rashin ladabi ga alkalin wasa.
Ita kuwa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) an ci ta tarar dalar Amurka 300,000 saboda rashin ladabin magoya baya, sannan aka sake cin ta tarar dalar Amurka 300,000 saboda rashin ladabina ’yan wasa da jami’an fasaha.
An ƙara ci tarar dalar Amurka 15,000 saboda ’yan wasa biyar sun samu jan kati a wasan.
A bangaren Maroko kuwa, CAF ta dakatar da dan wasan baya Achraf Hakimi daga wasanni biyu na CAF, daya daga cikin wasannin an dakatar da shi na shekara guda. Dan wasan tsakiya Ismaël Saibari ya samu dakatarwa daga wasanni uku tare da tarar dalar Amurka 100,000.
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Maroko (FRMF) kuma an ci ta tarar dalar Amurka 200,000 saboda rashin ladabin ’yan kwallo masu kawo kwallo a filin wasa, sannan aka sake cin ta tarar dalar Amurka 100,000 saboda ’yan wasa da jami’an fasaha sun mamaye wurin duba na’urar VAR.
An kuma ƙara cin Marokon tarar dalar Amurka 15,000 saboda amfani da “laser” daga magoya bayan Morocco.
Wasan karshe da aka buga a filin Stade Mohammed V da ke birnin Rabat ranar 18 ga Janairu 2026 ya rikide zuwa rikici a ƙarshe.
Bayan an soke kwallon Senegal saboda satar gida, na’urar VAR ta ba Maroko bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 98.
Kocin Senegal, Pape Thiaw, ya jagoranci ’yan wasansa suka bar fili a matsayin nuna rashin amincewa, lamarin da ya jawo rikici.
Bayan jinkiri na tsawon mintuna da dama, Senegal ta dawo filin, kuma mai tsaron raga Édouard Mendy ya cece ta a bugun daga kai sai mai tsaron raga na Marokon.
A ƙarin lokacin da aka yi, Pape Gueye ya zura kwallo a minti na hudu, wanda ya ba Senegal nasarar lashe kofin AFCON na 2025.
CAF ta kuma yi watsi da korafin da Ƙungiyar Maroko ta shigar kan karya dokokin gasar da Ƙungiyar Senegal ta yi, tana mai cewa babu hujja da ta tabbatar da hakan.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link