An jiyo karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman babban birnin Nijar
[ad_1]
An jiyo karar harbe-harbe da fashe-fashe masu karfi da safiyar Alhamis a kusa da filin jirgin saman kasa da kasa na diori hamani da ke Niamey, babban birnin Nijar.
Mazauna yankin sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP), cewa daga bisani an daina jink arar harbe-harben.
Bidiyoyin da mazauna yankin suka dauka sun nuna haske a sararin sama tare da karar fashe-fashe, yayin da wasu hotuna suka nuna wuta mai tsawo da motoci da suka ƙone.
Filin jirgin saman Diori Hamani na birnin Niamey na dauke da sansanin rundunar sojin saman kasar, kuma yana da nisan kilomita 10 daga fadar shugaban kasa.
Nijar, ƙasar da ke fama da hare-haren ’yan bindiga masu ikirarin jihadi a kai a kai, kuma tana ƙarƙashin jagorancin Abdourahamane Tiani sama da shekaru biyu, bayan ya kifar da gwamnatin farar hula a 2023.
Mazauna yankin sun ce harbe-harben sun fara ne da misalin ƙarfe 12 na dare, sannan suka lafa bayan kusan sa’o’i biyu.
Ba a tabbatar da abin da ya jawo harbe-harben ba, ko kuma ko akwai wadanda suka jikkata a ciki.
An kuma ji karar motoci masu kashe gobara suna nufar filin jirgin a farkon safiyar ranar, a cewar mazauna yankin.
Wani dan gwagwarmaya a shafukan sada zumunta mai goyon bayan mulkin soja, Ibrahim Bana, ya wallafa bidiyo a dandalin Facebook inda ya kira jama’a su fito kan tituna domin abin da ya kira da “kare ƙasar.”
Babban filin jirgin saman kasa da kasa na ƙasar shi ne hedkwatar rundunar haɗin gwiwa da Nijar da Burkina Faso da Mali suka kafa domin yaƙi da ƙungiyoyin jihadi masu tayar da tarzoma a yankin.
Tun bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum, shugabannin sojin Nijar sun kori dakarun Faransa daga kasar su gaba daya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link