Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaryata Zargin Biyan Boko Haram Kuɗin Fansa Kafin Sako Ɗaliban Neja

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta musanta rahoton da ke cewa ta biya Boko Haram kuɗin fansa domin a saki ɗaliban makarantar St. Mary da aka sace a Jihar Neja.

Rahoton ya fito ne daga kamfanin dillancin labarai na AFP, wanda ya ce wasu majiyoyi sun nuna an biya kuɗaɗe masu yawa kuma an saki wasu kwamandojin ƙungiyar kafin a sako ɗaliban.

  • Sufeto-Janar Na ‘Yansandan Nijeriya Kayode Egbetokun, Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa
  • Atiku Abubakar Ya Zargi Bola Tinubu Da Raunana Dimokuraɗiyya

A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta ce zargin ƙarya ne marar tushe, kuma ba a biya ko sisi ba, haka kuma ba a saki wani ɗan ta’adda ba.

Ta ƙara da cewa irin waɗannan rahotanni na iya rage ƙwarin gwiwar jami’an tsaro.

An sace ɗalibai da malamai sama da 260 a makarantar St. Mary da ke Papiri a watan Nuwamban 2025, kafin a sake su a rukuni-rukuni zuwa watan Disamban bara.

Rahoton ya kuma danganta yarjejeniyar da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, amma jami’an gwamnati sun ce sun sha musanta biyan kuɗin fansa a lokuta daban-daban.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *