Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 29 a Neja
[ad_1]
Aƙalla mutum 29 sun rasu a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a gabar kogin Malale da ke cikin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa, kwale-kwalen wanda ke ɗauke da fasinjoji 90, ya tashi ne daga Tugan Sule da ke yankin Shagunu, inda ya nufi Dugga domin zuwa wata ta’aziyya.
Majiyoyi sun bayyana cewa cikin waɗanda suka mutu har da mata da ƙananan yara, kuma zuwa yanzu an gano gawarwaki 29, yayin da aka ceto mutum 50 da ransu, sai kuma wasu mutum biyu da har yanzu ake ta ƙoƙarin lalubo su.
Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, wanda Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Haka kuma, wani babban jami’in Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa na Ƙasa (NIWA) a yankin, Akapo Adeboye, ya tabbatar da hakan ta wayar tarho.
A cewar Daraktan NSEMA: “Mun samu rahoton hatsarin kwale-kwale a wani gari mai suna Gausawa da ke yankin Malale a Borgu.
“Bisa bayanan da muka samu, kwale-kwalen ya tashi daga Tugan Sule da ke cikin gundumar Shagunu wanda yake ɗauke da mutum 90 ciki har da mata da yara, da nufin zuwa gaisuwar rasuwa a Dugga.
“Wannan lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, a sanadiyar lodin fasinjoji fiye da ƙima sannan kuma kwale-kwalen ya ci karo wani da kututturen itace.”
Ya ƙara da cewa jami’ai na ci gaba da aikin ceto domin gano waɗanda suka bace.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link