‘PENGASSAN ta amince ta janye yajin aiki kan rikincinta da matatar Dangote’
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta ce Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta amince da janye yajin aikin da take yi, bayan zaman sulhun kwanaki biyu da aka gudanar tare da shugabannin matatar man Dangote.
Zaman sulhun da aka gudanar a ranakun 29 da 30 ga Satumba, 2025, ya gudana ne a karkashin jagorancin Ministan Kwadago da samar da Ayyukan Yi, Dr. Mohammed Maigari Dingyadi, tare da halartar manyan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, da wakilan kungiyoyin kwadago.
A cikin sanarwar da aka fitar bayan kammala zaman, Minista Dingyadi ya ce yajin aikin na PENGASSAN ya biyo bayan sallamar ma’aikata sama da 800 daga matatar man Dangote.
Ministan ya ce, “Shugabannin PENGASSAN sun bayyana cewa umarnin dakatar da samar da gas ga kamfanin Dangote da kuma janye ayyuka ya biyo bayan sallamar sama da mambobi 800”.
A nasa bangaren, shugabancin kamfanin na Dangote, ya ce sallamar ma’aikatan ya faru ne sakamakon “gyare-gyaren da ake gudanarwa a cikin kamfanin.”
Bayan doguwar tattaunawa, bangarorin biyu sun cimma matsaya.
A cewar Ministan, “shugabancin kamfanin Dangote zai fara daukar matakin mayar da ma’aikatan da aka sallama zuwa wasu kamfanoni da ke karkashin rukunin kamfanoninsa ba tare da sun rasa albashinsu ba.”
Sanarwar ta kuma jaddada cewa ba za a ci zarafin kowanne ma’aikaci ba saboda rawar da ya taka a cikin rikicin.
Dangane da hakkokin kungiyoyin kwadago, Dingyadi ya tabbatar da cewa “yin kungiya hakki ne na ma’aikata bisa dokokin Najeriya, kuma dole ne a mutunta wannan hakki.”
Ya kara da cewa PENGASSAN ta amince ta fara aiwatar da janye yajin aikin da zuciya daya
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link