Makusanci Ya Yi Garkuwa Da Ɗan Shekara 4 Tare Da Masa Kisan Gilla A Bauchi Bayan Amsar Kuɗin Fansa
[ad_1]
Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta kama wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Rabiu Safiyanu, bisa zarginsa da yin garkuwa da kashe wani ƙaramin yaro ɗan shekara 4 a duniya mai suna Yunusa Salisu.
Mahaifin yaron Malam Salisu Yunusa, mazaunin unguwar Nasarawa Madina Quarters a cikin garin Bauchi ne ya kai rahoton ɓacewar ɗan nasa ga ‘yansanda a ranar 21 ga Maris. Ya ce sun nemi yaron nasu tun ranar 18 ga watan Maris sun rasa.
- Burina Na Gaba Bayan Fim Shi Ne Aure —Khadija
- Harin Bam A Maiduguri: Har Yanzu Akwai ’Yan Ƙunar Baƙin Wake Biyu Da Suka Yi Ɓatan Dabo – Zulum
A cewar mahaifin, su na wannan halin kuma sai ya samu ƙiran waya a ranar 19 ga Maris daga wani mutum ta wata lamba a ɓoye, inda aka buƙaci ya biya kuɗin fansa na N500,000. Ya ce ya biya N100,000 domin ganin an saki ɗansa, amma duk da biyan kuɗin ba a sako ɗan nasa ba.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Bauchi (PPRO), SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa jami’an bincike daga caji ofis ɗin ‘C’ Division, ƙarƙashin jagorancin babban Baturen ɗansanda (DPO), sun fara bincike bayan samun rahoton.
Binciken ya kai ga kama Rabiu Safiyanu, mai shekaru 20, wanda ke zaune a addreshi guda da mahaifin yaron, kuma aboki ne ga ƙanin mai koken ɓacewar ɗansa. Kasancewarsa abokin ƙanin mahaifin yaron ya ba shi damar shiga gidan a duk lokacin da ya ke so cikin sauƙi.
‘Yansanda sun ce wanda ake zargin ya amsa laifin ɗaukar yaron, ya shake shi, ya jefar da gawar a tsaunukan Warinje, sannan ya nemi ƙarin kuɗin fansa, bayan wanda ya amsa daga fari.
Daga bisani, ‘yansanda sun gano gawar yaron wadda ta fara ruɓewa, tare da alamun an shaƙe shi. Haka kuma an samu igiya da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata wannan ɗanyen aikin.
Jami’in da ke kula da asibitin ‘yansanda ya tabbatar da mutuwar yaron. An ɗauki hotunan gawar kafin daga bisani a miƙa ta ga iyalansa, inda aka binne ta nan take saboda dalilan kiyaye lafiyar jama’a.
SP Nafiu Habib ya ƙara da cewa wanda ake zargin yana hannun ‘yansanda domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ya karɓi kes ɗin domin tabbatar da cikakken bincike cikin gaggawa da kuma gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.
Ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga ‘yansanda domin samun damar daukan matakan gaggawa a duk lokacin buƙatar hakan.
[ad_2]
Source link